Amurka da Iran: Najeriya Ta Zamo Ta 1 a Kara Kudin Man Fetur
- Rahoton MEMAN ya nuna cewa Najeriya ce ta fi kowace ƙasa a Afirka samun tashin farashin fetur a wata shidan farkon shekarar 2026 da 39.5%
- Ƙungiyar ta danganta hauhawar farashin da yaƙin Isra'ila, Iran da Amurka wanda ya haddasa tashin farashin danyen mai da matsalar jigilar man fetur
- Duk da haka, rahoton MENAN ya ce matatar Dangote ta taimaka wajen rage dogaron Najeriya kan shigo da fetur daga ƙasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Najeriya ta zama ƙasar da ta fi kowace ƙasa a nahiyar Afirka fuskantar tashin farashin fetur a watann shida na farkon shekarar 2026.
Sabon rahoton Ƙungiyar Manyan Masu Kasuwancin Makamashi ta Najeriya (MEMAN) ya nuna cewa farashin fetur ya tashi da 39.5%, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila, Iran da Amurka.

Source: Getty Images
Punch ta rahoto cewa rikicin ya jawo tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya tare da ƙara tsadar jigilar kayan man fetur.
Dalilin tashin farashin fetur
Rahoton MEMAN na watan Janairu zuwa Yunin 2026 ya bayyana cewa rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar da fargabar ƙarancin mai a kasuwannin duniya.
A cewar ƙungiyar, farashin danyen mai ya haura dala 100 kan kowace ganga, yayin da jiragen dakon mai suka daina amfani da mashigar Hormuz, suka koma zagayawa ta Cape of Good Hope.
Rahoton ya ce hakan ya ƙara tsawon lokacin jigilar mai daga kusan kwanaki 18 zuwa kusan kwanaki 40.
MEMAN ta ce:
"Saboda tsarin kasuwar fetur da aka sassauta a Najeriya, hauhawar farashin da aka samu a kasuwannin duniya ta shafi masu sayen fetur kai tsaye."
"Najeriya ta samu tashin farashin fetur da 39.5%, wanda shi ne mafi tsada a Afirka, kuma ya ninka abin da wasu ƙasashe irin su Masar suka samu."
Dangote ya rage shigo da fetur
Duk da hauhawar farashin, MEMAN ta ce an samu gagarumin sauyi a bangaren tace man fetur a Najeriya.
Rahoton ya nuna cewa matatar Dangote ta taka muhimmiyar rawa wajen rage dogaro da fetur da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.
A cewar MEMAN, kaso na fetur da ake tacewa a cikin gida ya ƙaru daga 38.9% a shekarar 2025 zuwa 81.7% a farkon rabin shekarar 2026.

Source: Getty Images
Haka kuma, matatun cikin gida sun samar da kusan 64% na dizal da ake bukata, yayin da masana'antun sarrafa iskar gas suka samar da sama da 90%.
Farashin mai ya fara sauka
A wani labarin, mun ruwaito cewa farashin danyen mai ya faɗi da sama da 5% bayan Amurka da Iran sun dakatar da kai wa juna hare-hare bayan kusan makonni biyu na rikici.
Rahotanni sun nuna cewa farashin Brent ya sauka zuwa dala 91.80 kan kowace ganga, yayin da WTI ya sauka zuwa dala 84.47.
Jami'an Amurka sun bayyana cewa an dakatar da hare-haren ne domin ba diflomasiyya damar samar da mafita, duk da cewa an ci gaba da tura ƙarin sojoji zuwa yankin.
Asali: Legit.ng

