Takarar Sheikh Pantami a Jihar Gombe Ta Samu Gagarumin Goyon Baya gabanin Zaben 2027
- Daya daga cikin wadanda suka nemi takarar gwamnan Gombe a PDP, Hon. Monica Yahaya Khalto ta janye daga karar da aka shigar a kotu
- 'Yar siyasar ta kuma bayyana cikakken goyon bayanta ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a zaben gwamnan Gombe na 2027
- Ta ce ta dauki matakin ne bisa shawarar Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo domin hadin kan jam'iyya PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - 'Daya daga cikin masu neman takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam'iyyar PDP, Hon. Monica Yahaya Khalto, ta sanar da janyewa daga karar da suka shigar gaban kotu.
Hon. Monica ta tabbatar da tsame kanta daga karar da wasu masu neman takarar gwamna suka shigar domin kalubalantar sakamakon zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP a Gombe.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gidauniyar Farfesa Isa Sli Psntami ta wallafa a shafinta na Facebook yau Asabar, 18 ga watan Yuli, 2026.
Hakazalika, Monica Yahaya Khalto ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga dan takarar gwamnan PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Ta yi alkawarin yin aiki tukuru domin ganin ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027.
Dalilin janyewar Hon Monica Yahaya
Monica ta bayyana cewa ta dauki matakin ne bayan tuntuba da kuma girmama rokon jagoran PDP a jihar Gombe, tsohon gwamna Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda ya bukace ta da ta janye daga shari'ar domin tabbatar da hadin kan jam'iyya.
Ta bayyana Dankwambo a matsayin uba kuma jagora wanda take matukar girmama shawararsa.
A cewarta, ta amince da wannan shawara ne saboda hadin kan PDP da ci gaban jihar Gombe sun fi muhimmanci fiye da burin mutum daya.
Ta kara da cewa ya kamata dukkan mambobin jam'iyyar su ci gaba da mayar da hankali wajen tabbatar da nasarar PDP a zaben 2027 domin samar wa al'ummar jihar Gombe ingantaccen shugabanci.
Pantami ya yabawa Monica
A nasa bangaren, tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna matukar godiyarsa ga Hon. Monica Yahaya Khalto saboda abin da ya bayyana a matsayin nuna kishin kasa da kuma jajircewa wajen tabbatar da hadin kan PDP.

Kara karanta wannan
Gwamna Kefas ya ajiye mataimakinsa, ya zabi mace a matsayin abokiyar takara a 2027
Ya tabbatar mata cewa har yanzu tana daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar, yana mai cewa za a tafiyar da kowa tare domin gina PDP mai karfi da kuma kyakkyawar makoma ga jihar Gombe.

Source: Facebook
Pantami ya kai mata ziyara
A matsayin nuna girmamawa da godiya, Farfesa Pantami ya kai wa Monica Yahaya Khalto ziyara a gidanta domin gode mata bisa goyon bayan da ta nuna da kuma matakin da ta dauka.
Ya bayyana janyewar tata daga shari'ar a matsayin sadaukarwa da aka yi domin maslahar PDP da kuma al'ummar jihar Gombe baki daya.
Pantami ya fara jefa maganganu a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya zargi masu rike da madafun iko a yau da handame dukiyar al’ummar da aka ba su amana.
Dan takarar gwamnan jihar Gombe na PDP, Pantami ya ce masu ganin akwai yiwuwar a murde zaben 2027, sun jahilci wayewar al’ummar yau kuma ba su san dokar kasa ba.
Asali: Legit.ng
