'Yan Kasuwa Sun Rage Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

'Yan Kasuwa Sun Rage Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

  • Masu sayar da man fetur sun rage farashin fetur a manyan matatun ajiya da ke Legas, Warri, Fatakwal da Calabar
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan dillalai sun rage farashi da har N23 kan kowace lita domin jawo karin kwastomomi
  • Masana sun bayyana cewa karin tace man fetur a gida da kuma gasa tsakanin 'yan kasuwa ne suka haddasa saukar farashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – An samu saukar farashin man fetur a manyan matatun ajiya na Najeriya bayan 'yan kasuwa sun rage farashi da har N23 kan kowace lita a wasu wurare.

Saukar farashin ya shafi manyan cibiyoyin samar da fetur da ke Legas, Warri, Calabar da Fatakwal, lamarin da ke nuna karuwar gasa tsakanin dillalan man fetur.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno

Ana saka man fetur a gidan mai
Wani mai mota na sayen fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta rahoto cewa babu wani rumbun ajiya ajiya da ya kara farashin fetur, yayin da mafi yawan su ko dai sun rage farashi ko kuma sun ci gaba da sayarwa da tsohon farashi.

Yadda farashin mai ya sauka

A Legas, matatar Dangote ta ci gaba da sayar da fetur kan N1,216 kowace lita, wanda shi ne mafi ƙarancin farashi a cikin manyan masu samar da fetur.

Kamfanin Pinnacle ya rage farashinsa da N2 zuwa N1,216 kan kowace lita, yayin da MRS ya sauke nasa zuwa N1,222 bayan rage N2.

Shi ma Emadeb ya rage N7 zuwa N1,218, yayin da kamfanonin Aiteo, Nipco, Ascon, Shema da T-Time suka ci gaba da sayar da fetur tsakanin N1,218 zuwa N1,220 kan kowace lita.

An samu ragin N23 a Warri

A Warri kuwa, kamfanonin Bulk Strategic, Liquid Bulk, Masters, Matrix da Sigmund sun rage farashin fetur zuwa kusan N1,245 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Farashin mai ya sauka sosai bayan dakatar da yakin Amurka da Iran

Rain Oil ya yi daya daga cikin manyan ragin farashi inda ya rage N23 zuwa N1,245 kan kowace lita, yayin da Matrix ya rage N10 zuwa irin wannan farashin.

A Calabar, kamfanin Northwest ya rage N15 zuwa N1,235 kan kowace lita, Mainland ya sauke N10 zuwa N1,240, yayin da Hong Petroleum ya rage N2 zuwa N1,233, wanda shi ne mafi ƙarancin farashi a yankin.

A Fatakwal kuma, Matrix ya rage N3 zuwa N1,243, Optima ya rage N2 zuwa N1,243, yayin da Rain Oil ya sake rage N23 zuwa N1,245 kan kowace lita.

Matatar da Dangote ya gina a Legas
Matatar Aliko Dangote da ke tace mai a Najeriya. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Masana sun bayyana cewa wannan saukar farashi na nuna ingantuwar wadatar man fetur da kuma karuwar gasa tsakanin 'yan kasuwa domin jawo masu saye da yawa.

Sun kuma ce duk da raguwar farashin a matatun ajiya, farashin da masu amfani za su biya a gidajen mai zai dogara ne da kudin sufuri, ribar 'yan kasuwa da sauran kudin gudanar da aiki.

Mai ya fi tsada a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Najeriya ce ta fi kowace kasa a Afirka fuskantar tashin farashin fetur a farkon shekarar 2026.

Kara karanta wannan

An bayyana yadda Yariman Saudiyya Abdullah bin Fahad ya rasu a otal din Landan

Rahoton kungiyar MEMAN ya nuna cewa farashin fetur ya karu da kashi 39.5 cikin 100 sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila, Iran da Amurka.

Kungiyar ta bayyana cewa rikicin ya dagula harkokin jigilar danyen mai ta mashigar Hormuz, lamarin da ya sa kudin jigilar man fetur ya karu sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng