Bayan Ficewarsa daga Takara a APC, Yan Pantamiyya Sun Bar Pantami, Sun Bi Jamilu
- Kungiyar Pantamiyya Movement Brotherhood mai goyon bayan Farfesa Isa Pantami ta fice daga ci gaba da zama a bangaren tsohon ministan
- Pantamiyya ta bayyana goyon bayanta ga Jamilu Isyaku Gwamna bayan zaben fitar da gwani na APC a Gombe da ya samu nasara a watan nan
- Jamilu Gwamna ya samu kuri’u 247,161 wajen kayar da Pantami da Saidu Alkali, duk da cewa an samu sabani kafin gudanar da zaben fitar da gwanin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pantami, Gombe - Kungiyar Pantamiyya Movement Brotherhood ta bayyana shirin goyon bayan zababben dan takarar APC a jihar Gombe.
Kungiyar da ke biyayya ga tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamnan APC a Gombe, Jamilu Isyaku Gwamna.

Source: Facebook
Shugaban kungiyar, Sanusi Hamisu Usman, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar nuna goyon baya da suka kai wa Gwamna, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Yadda aka fi ƙarfin gwamnan Kwara kan tsayar da magajinsa, aka zaɓi kakakin majalisa
Gombe: Yadda aka yi zaben fitar da gwani
Gwamna ya lashe zaben fitar da gwani na APC bayan samun kuri’u 247,161 inda ya doke Pantami da ya samu kuri’u 12,120 da kuma Saidu Ahmed Alkali da ya samu 11,612.
Tun farko jam’iyyar APC ta zabi Gwamna a matsayin dan takarar hadaka, amma Pantami da Alkali sun nuna rashin amincewa wanda ya sa aka gudanar da zaben fidda gwani.
Daga baya Pantami ya janye daga takarar, yana zargin an karya dokar zabe ta 2026 tare da rashin samar da hanyoyin sadarwa masu inganci a jam’iyyar.

Source: Twitter
Dalilin Pantamiyya na komawa layin Gwamna
Sai dai duk da janyewar Pantami daga takarar, kungiyar Pantamiyya Movement Brotherhood ta bayyana cewa za ta marawa Gwamna baya domin hadin kan jam’iyya.
Shugabanta ya ce kungiyar na da masu gudanarwa sama da 100 a dukkan mazabu da kananan hukumomi 11 na jihar Gombe.
A cewarsa, kungiyar ta yanke shawarar goyon bayan Gwamna ne saboda yadda yake samun karbuwa a cikin APC da kuma tsakanin talakawan jihar.

Kara karanta wannan
Gwanna Alia ya tika mutum 2 da kasa, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a zaben 2027
Sanusi ya ce suna son tabbatar da APC ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya tare da samun gagarumar nasara a zabukan 2027.
Ya kuma roki Pantami da sauran ‘yan takarar gwamna na APC su hada kai da Gwamna domin ci gaban jam’iyya da jihar Gombe baki daya.
Da yake martani, Gwamna ya yabawa kungiyar bisa fifita hadin kan jam’iyya, yana mai cewa hakan alama ce ta balagar siyasa da kishin APC.
Gwamna ya kuma jaddada kudirinsa na tara goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dukkan ‘yan takarar APC a zaben 2027, cewar Leadership.
'Dan Pantami ya magantu kan takarar mahaifinsa
Mun ba ku labarin cewa 'dan tsohon ministan a Najeriya, AbdulRahman Isa Pantami ya yi gyara a rahotannin da ke cewa mahaifinsa, Isa Ali Pantami ya hakura da neman takara.
A ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2026 ne aka samu rahotannin da suka ce Farfesa Ali Pantami ya hakura da batun neman takarar gwamna a Gombe.
A karin bayanin da ya fitar, AbdulRahman Isa Pantami ya yi karin haske game da batun, inda ya bayyana cewa maganar neman takarar gwamna na nan.
Asali: Legit.ng