Sojojin Sama Sun Yi Barin Wuta kan Yan Ta’adda, Miyagu da Dama Sun Rasa Rayukansu

Sojojin Sama Sun Yi Barin Wuta kan Yan Ta’adda, Miyagu da Dama Sun Rasa Rayukansu

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe mayakan ISWAP guda takwas a wani samamen sama da suka kai yankin Timbuktu Triangle, Borno
  • Harin ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri kan ‘yan ta’addan da suka taru a Thethangala, suna shirin kai hari kan sojojin Najeriya
  • Rundunar soji ta ce yanayin tsaro ya kasance cikin kwanciyar hankali amma babu tabbas, yayin da Operation Hadin Kai ke ci gaba da kai hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe wasu mayakan kungiyar Islamic State West Africa Province, ISWAP, guda takwas a wani samamen sama da aka kai Borno.

An kai harin ne a yankin Timbuktu Triangle, bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu ‘yan ta’adda sun taru a Thethangala.

Sojojin sama sun hallaka yan ISWAP a Borno
Jirgin saman sojojin Najeriya na barin wuta. Hoto: Nigeria Airforce.
Source: Getty Images

Yan ISWAP 8 sun mutu a Borno

Kara karanta wannan

Sojoji sun sauya taku, an tura zazzafan gargadi ga 'yan ta'adda

Wani rahoto daga shafin masanin yaki da ta’addanci na Zagazola Makama ya ce an gudanar da aikin da misalin karfe 9:56 na dare ranar 18 ga Agusta.

Rahoton ya ce wani jirgin sama mai suna Guardian ya fara gano inda ‘yan ta’addan suke kafin a kai musu harin da aka tsara da tsanaki.

Majiyoyi sun bayyana cewa jirgin ya gano ‘yan ta’adda guda takwas a wuri guda, inda suke kwance suna jiran lokacin fara kai hari kan sojojin Najeriya.

Bayan gano su, rundunar sojin ta kai musu harin sama na musamman, inda rahoton tantance sakamakon harin ya nuna cewa an hallaka dukkan ‘yan ta’addan.

An hallaka yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno da aka kashe yan kungiyar ISWAP. Hoto: Legit.
Source: Original

Sojoji sun tarwatsa tasirin yan ISWAP

Rahoton ya kara da cewa ba a sake ganin wani motsi a yankin ba bayan harin, lamarin da ke nuna nasarar aikin sojin.

Yankin da aka kai harin na daga cikin muhimman wuraren da ake ganin kungiyar ISWAP na gudanar da ayyukanta a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Babban kwamandan sojin Najeriya ya ce yanayin tsaro a yankin yana cikin kwanciyar hankali, sai dai har yanzu akwai rashin tabbas game da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza da Lakurawa 300, an rasa rayuka bayan yin jina jina

Ya kuma bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai na ci gaba da nuna kwazo da inganci wajen gudanar da ayyukan yaki da ‘yan ta’adda.

A halin yanzu, Operation Hadin Kai ta kara tsananta ayyukan hadin gwiwa na sama da kasa domin fatattakar kungiyoyin ‘yan ta’adda da lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki.

Ayyukan sun fi mayar da hankali kan wuraren da ‘yan tada kayar baya ke kokarin sake taruwa da kuma shirya kai hare-hare kan sansanonin sojoji, cewar TheCable.

Fasto ya ce addu'a zai magance matsalar tsaro

Kun ji cewa wani Fasto Oliver Dashe na Maiduguri ya bukaci Kiristoci su kara dagewa da addu’a domin taimaka wajen murkushe Boko Haram.

Ya ce Borno ta samu zaman lafiya amma gwamnati da jama’a su ci gaba da kokarin tabbatar da cikakken nasara.

Bishop Dashe ya kuma bukaci gwamnati ta tarayya da jihohi su tallafa wa jami’an tsaro domin shiga dazuka da tsaunuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.