"Ban Nemi Zama Mataimakin Atiku ba": An Fusata Rotimi Amaechi da Tambayar Tikitin ADC
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce bai sayi fom domin ya zama mataimakin shugaban kasa ba a zaben 2027 a inuwar jam'iyyar ADC ba
- Amaechi ya nuna rashin jin dadinsa kan rade-radin cewa zai iya zama abokin takarar Atiku Abubakar a jam’iyyar ADC yayin da jam'iyyar ke shirin tunkarar zabe
- Martanin ‘yan Najeriya ya nuna yadda ake samun sabani da cacar baki tsakanin masu neman tikitin shugaban kasa a ADC kafin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Mai neman tikitin shugaban kasa a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa bai sayi fam domin neman kujerar mataimakin shugaban kasa ba a zaben 2027.
Amaechi ya nuna rashin jin dadinsa kan rade-radin cewa zai iya zama abokin takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a karkashin jam’iyyar ADC.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma tsohon ministan sufuri ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust TV ranar Litinin, 17 ga watan Mayun 2026.
Amaechi ya yi watsi da zama mataimakin Atiku
Jaridar The Nation ta labarto cewa yayin da ake tattaunawa kan rikicin neman tikitin shugaban kasa a ADC, Amaechi ya yi martani mai zafi kan batun cewa zai iya zama mataimakin shugaban kasa.
Ya ce:
“Ka daina wannan maganar banza. Ban sayi fam domin zama mataimakin shugaban kasa ba.”
Ya kara da cewa:
“Kada ka sake fadar hakan.”

Source: Twitter
Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ‘yan Najeriya suka goyi bayansa, yayin da wasu suka soki yadda ya mayar da martani.
Ra'ayoyi sun saba kan takarar Amaechi
Wasu 'yan Najeriya sun yi martani ga batun ko tsohon minista, Rotimi Amaechi zai iya zama abokin takarar Atiku Abubakar a babban zabe mai zuwa.
Wani mai amfani da kafar X mai suna @OzumbaPros7380 ya ce:
“Masu goyon bayan Atiku kullum rokon mutane suke yi su zama mataimakinsa. Da zarar ka ki, sai su dauke ka a matsayin makiyi. Sun roki Obi da Amaechi. Lokaci ya yi da Atiku zai janye kansa don kare mutuncinsa.”
Wani @fspevent ya ce:
Ya ce:
“A gare ni, amsarsa ba ta yi kama da ta mutumin da yake da halin shugabanci ba, kuma abin takaici ne.”
Amaechi ya mika fam na takara ga ADC
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya mika fam dinsa na neman takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar ADC gabanin babban zabe mai zuwa.
Rotimi Amaechi, wanda tsohon gwamna ne ya bayyana lokacin da zai kwashe wajen gyara Najeriya idan har mutanen kasar nan za su amince, su kuma ba shi dama a zaben da za a yi a shekarar 2027.
Hakazalika, tsohon ministan ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta daga cikin masu neman darewa kan madafun ikon kasar nan, domin yana da hanyar da zai kawo gyara a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

