Atiku Abubakar da Gaske Yake Yi kan Batun Neman Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

Atiku Abubakar da Gaske Yake Yi kan Batun Neman Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

  • Wani lauya mai fafutukar kare hakkin bil'adama, Inibehe Effiong ya nemi karin haske kan batun takarar Atiku Abubakar a zaben 2027
  • Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa, Paul Ibe ya ce Atiku da gaske yake yi kuma ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki
  • Ya ce idan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa na ADC, zai bukaci goyon bayan ‘yan Najeriya domin kayar da gwamnatin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya jaddada aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2027.

Mai ba Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa ubangidansa na da cikakken niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Ban nemi zama mataimakin Atiku ba": An fusata Rotimi Ameachi da tambayar tikitin ADC

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yana jawabi a wurin taro a Abuja Hoto: @atiku
Source: Facebook

Ibe ya bayyana hakan ne ranar Talata ta shafinsa na X yayin da yake mayar da martani ga wata tambaya da lauya mai kare hakkin bil’adama kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Inibehe Effiong, ya yi.

Effiong ya jefa tambaya cewa: “Shin Atiku da gaske yana da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027?”

Atiku na tattaunawa da shugabannin ADC

Da yake mayar da martani ga lauyan, Paul Ibe ya ce Atiku yana tattaunawa da shugabanni, masu ruwa da tsaki da kuma mambobin jam’iyyar ADC kan yiwuwar takararsa.

“Eh, Atiku da gaske yake, yana da cikakken niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. A yanzu haka yana tattaunawa da shugabanni, masu ruwa da tsaki da mambobin ADC kan batun takararsa,” in ji Ibe.

Ya kara da cewa idan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, zai bukaci goyon bayan ‘yan Najeriya domin kayar da gwamnatin APC karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya magantu kan 'barazanar' Jonathan ga takararsa da Kwankwaso

Ya caccaki gwamnatin Tinubu

Ibe ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa Najeriya cikin mawuyacin hali na matsin rayuwa tun bayan kafa ta a 2023.

Ya ce:

“Tambayar ita ce, shin ‘yan Najeriya sun shirya barin bautar da Tinubu ya mayar da kasar nan ta ci gaba?”
Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a wurin taron kaddamar da hadaka a ADC Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Ana shirin zaben fitar da gwani na ADC

Jam’iyyar ADC ta sanya ranar 23 ga watan Mayu, 2026 domin gudanar da zaben tsaida gwani na shugaban kasa, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Ana sa ran Atiku zai fafata da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da kuma tsohon ma’aikacin banki kuma masanin tattalin arziki, Alhaji Mohammed Hayatu-Deen.

Atiku ya maida fam din takara a ADC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, sun miƙa fom ɗin neman tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Atiku ya ce takararsa ta shugaban ƙasa tana wakiltar wani gagarumin yunƙuri na dawo da ci gaba da sake gina Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce batun takarar shi ta wuce batun siyasa kawai, ya ce tana da alaƙa da sabunta Najeriya da dawo da ci gabanta a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262