"Ba Dan Koyo ba"; Atiku Ya Gano Dan Takarar da Ya Cancanci Tutar ADC don Karawa da Tinubu a 2027

"Ba Dan Koyo ba"; Atiku Ya Gano Dan Takarar da Ya Cancanci Tutar ADC don Karawa da Tinubu a 2027

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya na shirin gudanar da zaben fitar da gwani domin tsayar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya aika da sako ga jam'iyyar kan dan takarar da ya kamata ta zaba
  • Atiku ya nuna cewa ana bukatar wanda ya san makamar aiki domin shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zaben fitar da gwani da jam'iyyar ADC za ta gudanar.

Atiku ya bayyana cewa dole ne jam'iyyar ADC ta tsayar da ɗan takara mai cancanta da gogewa wanda ke da ikon tunkarar ƙalubalen tattalin arzikin Najeriya da kuma durƙushewar hukumomi gabannin babban zaɓen 2027.

Atiku ya ba jam'iyyar ADC shawara
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa ga Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, 24 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Wace shawara Atiku ya ba ADC?

Atiku ya ce zaɓin da ke gaban wakilan ADC ya wuce batun siyasa kawai, inda ya bayyana shi a matsayin wani babban nauyi na tarihi.

A cewarsa, an kafa ADC ne a kan madaidaitan ginshiƙai na gaskiya, riƙon amana, haɗa kai, da kuma sabunta tsarin demokraɗiyya, inda ya jaddada cewa Najeriya tana buƙatar shugaba wanda ya shirya tsaf domin gudanar da mulki tun daga rana ta farko.

“Wannan ba lokaci ne na gwaje-gwajen siyasa ba. Najeriya ba za ta iya ɗaukar nauyin shugabancin ƙasa na koyon aiki a kan kujera ba.”

- Atiku Abubakar

Atiku ya fadi shugaban da Najeriya ke bukata

Atiku ya ba da hujjarsa cewa ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu suna buƙatar kwararren shugaba wanda aka riga aka gwada shi da gogewar aikin zartarwa, fahimtar tattalin arziki, da kuma karɓuwa a sassan ƙasa baki ɗaya.

“Najeriya a yau tana buƙatar shugaban ƙasa wanda ya fahimci mulki ba a matsayin ƙa'ida ta littafi ba, a'a, a matsayin babban nauyi na zahiri."

Kara karanta wannan

2027: Jam'iyyar ADC ta amince mutum 3 su nemi takarar shugaban kasa a Najeriya

“Tana buƙatar wanda ya taɓa yin tattaunawa a matakin duniya, ya samar da ayyukan yi ta hanyar kasuwanci da masana'antu, ya tafiyar da kofofin rikicin ƙasa, ya gina haɗin gwiwa, kuma ya kasance mai tsara kyakkyawar taswirar da za a iya amfani da ita domin farfaɗo da tattalin arziki da kuma sabunta ƙasa."

- Atiku Abubakar

ADC ta samu shawara wajen Atiku
Atiku Abubakar a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku na son a duba cancanta

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma buƙaci wakilan na ADC da su fifita cancanta akan ra'ayi yayin da jam'iyyar ke shirin fuskantar babban zaɓen shekarar 2027, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Ya ƙara da cewa yayin da wasu za su iya dogara a kan kalaman baki da muryoyi na yaƙin neman zaɓe, shi yana ɗauke da tarihin gudanar da hukumomi da kuma gogewar da ake buƙata domin jagoranci cikin inganci.

“Ba a lashe zaɓe akan karsashin dandalin sada zumunta kaɗai ba. Shugabanci ba wasan kwaikwayo ba ne. Kujerar shugabancin ƙasa ba dandalin yin wasa ba ne."
“Dole ne ADC ta gabatar wa ’yan Najeriya ɗan takararta mafi ƙarfi, mafi inganci, kuma mafi shiri, ba wai kawai wanda ya fi kowa surutu ba."

- Atiku Abubakar

An gargadi Atiku kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Satguru Mahraji ya ja kunnen Alhaji Abubakar kan yin takara a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon dan acaba da ya zama ɗan majalisa ya rasa takara bayan ya koma APC

Malamin dubar ya gargadi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan yin takarar zaben shekarar 2027 da ke kara matsowa.

Maharaji ya ce bai kamata Atiku ko sauran ‘yan Arewa su tsaya takara ba a 2027, inda ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar siyasa tsakanin Arewa da Kudu wadda ta tsara yadda ake musayar mulki domin tabbatar da daidaito a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng