Tsohon Dan Acaba da Ya Zama Ɗan Majalisa Ya Rasa Takara bayan Ya Koma APC

Tsohon Dan Acaba da Ya Zama Ɗan Majalisa Ya Rasa Takara bayan Ya Koma APC

  • Tsohon dan acabar nan da ya shiga siyasa, Donatus Mathew ya rasa tikitin takarar jam'iyya mai mulki ta APC bayan rabu wa da jam'iyyarsa ta LP
  • Donatus Mathew ya shahara bayan ya kayar da ɗan majalisa mai wa’adi huɗu a zaɓen 2023 a jihar Kaduna yayin da ya rabu da sana'ar acaba
  • Rahotanni sun nuna cewa kusan ‘yan majalisa 70 ba za su dawo Majalisar tarayya ba bayan zaɓen fitar da gwani da jam'iyyar APC ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Yayin da jam’iyyar APC ta kammala zaɓen fitar da gwani na sanatoci da ‘yan majalisar wakilai gabanin babban zaɓen 2027, alamu sun nuna cewa kusan ‘yan majalisa 70 na majalisa ta 10 ba za su samu damar koma wa ba.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, APC ta tsayar da 'dan takarar gwamna a jihar Gombe

Daga cikin fitattun sunayen akwai Donatus Mathew, tsohon dan acaba wanda ya taba jan hankalin jama’a bayan ya yi nasarar shiga majalisar wakilai daga jihar Kaduna.

Donatus Mathew ya rasa tikitin takara
'Dan majalisa Donatus Mathew da ya rasa tikitin takara a APC Hoto: Akai Son
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa APC na da kujeru 242 a majalisar wakilai da kuma kujeru 88 a majalisar dattawa, inda ‘yan majalisa da dama suka nemi tikitin sake tsayawa takara.

'Dan majalisar Kaura ya rasa takara a APC

Rahoton ya ce sai dai Mathew, wanda aka zaɓa a 2023 karkashin jam’iyyar LP domin wakiltar mazaɓar Kaura ta jihar Kaduna kafin daga baya ya koma APC, ya rasa tikitin jam’iyya mai mulki bayan zaɓen fitar da gwani.

Mathew ya fara shahara ne a lokacin zaɓen 2023 bayan ya kayar da ɗan majalisa da ke wa’adi na huɗu a mazaɓar Kaura da ƙuri’u 10,508 yayin da babban abokin hamayyarsa ya samu ƙuri’u 10,297.

An ɗauki nasararsa a matsayin alamar tasirin talakawa a siyasa musamman a lokacin da magoya bayan Peter Obi na LP suka mamaye fannoni da dama na siyasar ƙasar nan.

Donatus Mathew ya rasa tikitin takara bayan ya rabu da jam'iyyarsa ta LP
Taswirar jihar Kaduna inda Donatus Mathew ya fadi zaben fitar da gwanin APC Hoto: Legit.ng
Source: Original

An haifi Mathew a shekarar 1988 a Kpak da ke masarautar Kagoro a ƙaramar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta soke tsarin INEC, ta sauya lissafin babban zaben 2027 a Najeriya

Ya yi makarantar firamare ta LGEA a Kadarko kafin ya wuce makarantar Saint Jani Seminary da kuma Kwalejin Malamai ta Kagoro inda ya kammala karatun sakandare.

Yadda dan majalisar ya yi acaba kafin shiga siyasa

Kafin ya shiga siyasa ta ƙasa, Mathew ya kasance dan acaba, aikin da ya ce ya taimaka masa wajen rayuwa a lokacin matsin tattali da rashin aikin yi.

A wata hira da aka yi da shi, ya ce:

“Tun kafin na zama kansila, ni direban acaba ne. Da babur nake neman abinci kuma ina alfahari da hakan. Wannan shi ne asalin rayuwata.”

Mathew ya bayyana cewa ya shiga LP ne domin mara wa Peter Obi baya a takarar shugaban ƙasa kafin daga baya magoya baya da mutanen mazabarsa suka buƙace shi ya tsaya takarar majalisar wakilai.

Ya ce burinsa shi ne samar da shugabanci nagari tare da ƙarfafa wa talakawa guiwa cewa siyasa ba ta masu kuɗi kaɗai ba ce.

Sai dai a watan Disamban 2024 ya sauya sheka daga LP zuwa APC, yana mai danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida a LP da kuma buƙatar samar da daidaiton siyasa.

Kara karanta wannan

Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River

Sauya sheƙar tasa ta fusata wasu daga cikin magoya bayansa da suka yi imanin cewa LP ce da goyon bayan talakawa suka ba shi nasarar shiga majalisa a 2023.

'Dan majalisa a kano ya sauya sheka

A baya, kun samu labarin cewa jam’iyyar APC ta rasa ɗan majalisar jiha daga jihar Kano wanda ke wakiltar mazabar Gwale, yankin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito Tsohon gwamnan Kano.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tarbi sabon ɗan jam’iyyar a gidansa da ke Abuja tare da wasu sababbin 'yan jam'iyya a shirin da ake yi na tunkarar babban zaben 2027 da ke tafe a Najeriya.

Sauyin jam’iyyar ya biyo bayan hukuncin kotun tarayya da ya buɗe damar sauya sheƙa, yayin ADC ke hasashen karin ficewar mutane daga jam'iyya mai mulki ta APC a kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng