Dan Majalisa daga Mazabar Gwamna Abba Ya Bi Layin Kwankwaso zuwa NDC
- Jam’iyyar APC ta rasa ɗan majalisar jiha daga jihar Kano wanda ke wakiltar mazabar Gwale, yankin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito
- Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tarbi sabon ɗan jam’iyyar a gidansa da ke Abuja tare da wasu sababbin mambobi
- Sauyin jam’iyyar ya biyo bayan hukuncin kotun tarayya da ya buɗe damar sauya sheƙa, yayin ADC ke hasashen karin ficewar mutane daga APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Ɗan majalisar dokokin Kano mai wakiltar mazabar Gwale, Hon. Abdulmajid Isa Umar Mai Rigar Fata, ya tattara kayansa daga APC.
Hon. Abdulmajid Mai Rigar Fata ya sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar NDC mai adawa da Rabiu Kwankwaso ke ciki.

Source: Twitter
Abba ya rasa dan majalisa daga mazabarsa
Mai Rigar Fata na wakiltar ƙaramar hukumar Gwale, inda gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fito, kuma ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasar yankin, cewar Daily Trust.
An karɓe shi ne a ranar Alhamis ta hannun tsohon gwamnan Kano kuma jigo a NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Maitama a Abuja.
Kwankwaso ya bayyana cewa shigowar sababbin mambobin zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a matakin ƙasa da kuma tushen al’umma a Kano.

Source: Facebook
Sauran wadanda suka shiga NDC
An fara zaɓen Mai Rigar Fata a shekarar 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP mai alaƙa da Kwankwaso, kafin daga bisani ya bi gwamna Yusuf zuwa APC.
Sauya sheƙarsa na zuwa ne bayan ya gaza samun tikitin APC domin komawa majalisar dokokin Kano a zaɓen gaba mai zuwa.
Sauran waɗanda suka shiga jam'iyyar NDC sun haɗa da Hon. Kabiru Sani Auwal Obi, tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gwale, da Malam Mahadi Isa Umar.
Hadimin Kwankwaso, Saifullah Hassan ya wallafa rahoton a shafinsa na Facebook inda ya ce jagoran ya karbi dan majalisar a gidansa da ke Abuja.
Ya ce:
"Yau Alhamis, 21 ga Mayu, 2026, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya karɓi Hon. Abdulmajid Isa Umar Mai Rigar Fata, ɗan majalisar dokokin Kano mai wakiltar mazabar Gwale, bayan sauya sheƙarsa daga APC zuwa jam'iyyar NDC, a gidansa da ke Maitama, Abuja.
"Haka kuma ya karɓi Hon. Kabiru Sani Auwal Obi, tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gwale, da Malam Mahadi Isa Umar, waɗanda suka shiga jam’iyyar tare da shi."
Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan wata kotun tarayya ta ba da hukuncin da ya sake buɗe ƙofar sauya sheƙar siyasa da INEC ta taɓa takaita.
APC ta zabi Abba a matsayin dan takara
Tun farko, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bi tsarin maslaha domin zabar dan takararta na gwamna a zaben da za a gudanar a shekarar 2027
APC ta zabi Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda zai yi mata takarar gwamnan jihar Kano a zaben da ake tunkara a badi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa kan wannan amincewa da aka yi masa, ya yi alkawarin ci gaba da kawo romon dimokuradiyya.
Asali: Legit.ng

