"Ba Kwaya ba ce": Alhasan Doguwa Ya Fadi Abin da Ya Sauya Launin Harshensa a Taron APC

"Ba Kwaya ba ce": Alhasan Doguwa Ya Fadi Abin da Ya Sauya Launin Harshensa a Taron APC

  • 'Dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada a jihar Kano, Hon. Alasan Ado Doguwa ya musanta zargin amfani da miyagun ƙwayoyi
  • Ya yi martanin ne bayan wani hotonsa da aka ga launin harshensa ya sauya zuwa launin da ake zargin wata kwaya ce mai dagula hankalin masu amfani da ita
  • Doguwa ya bayyana cewa duk da bai san wadanda suka dauki hoton bisa zargin bata masa suna ba, amma zai dauki matakin da ya dace nan gaba kadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

Jihar Kano - Ɗan majalisar tarayya, Hon. Alasan Ado Doguwa, ya musanta zargin cewa yana ta’amali da miyagun ƙwayoyi bayan wani hotonsa da ya yi yawo, wanda ya nuna harshensa ya canja launi.

Kara karanta wannan

"Ana rasa abinci a gidana": Ministan Buhari, Amaechi ya magantu kan mulki a Najeriya

Hoton da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna harshen ɗan majalisar ya sauya launi zuwa shuɗi, lamarin da wasu suka danganta da amfani da wata ƙwaya da masu ta’amali da miyagun ƙwayoyi ke amfani da ita.

Alasan Ado Doguwa ya yi Allah Ya isa
'Dan majalisar wakilan Najeriya a zaman wakilai a Abuja Hoto: Alhassan Ado Doguwa
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da DCL Hausa, Alasan Ado Doguwa ya karyata zargin cewa ya sha wani abin maye kafin taron da aka gudanar a ƙasar Rano, yana mai cewa masu yi masa wannan kazafi ba za su ci banza ba.

Hon. Alasan Doguwa ya kare kansa

A hirar da ya yi, Hon. Alasan Ado Doguwa ya bayyana abin da ya sa aka ga harshensa ya sauya launi zuwa shuɗi a wani taron siyasa da gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarta a Kano.

Ya bayyana cewa shi mutum ne da ya saba amfani da alawar nan mai ɗan yaji wato Tom-tom saboda yawan mura, kuma a lokacin taron muryarsa ta ɗan sarke, hakan ya sa ya nemi a sayo masa alawar da ya saba amfani da ita.

Hon. Alasan Ado Doguwa ya ƙara da cewa:

“Taro ne wanda na alfarma da mutunta kai, maganar ka je da abin da ya shafi barna akwai mamaki a ciki. Ni bisa al’ada ta yau da kullum, na saba da shan Tom-Tom saboda yawanci bakina ba zai rasa mura ba. Na ɗauki alawar na sa a bakina kamar yadda na saba.”

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Ma'aikacin Aso Villa ya tona yadda aka shirya kutsa wa fadar shugaban kasa

Alhassan Ado Doguwa ya ce alawar ice mint ya sha aka ga sauyi a harshensa
Hon Alhassan Ado Doguwa, wakilin Tudunwada/Doguwa a majalisar wakilai @aadoguwa
Source: Twitter

Ya bayyana cewa lokacin da ya hau doki zuwa taron ƙaddamar da takarar Kawu Sumaila a Rano, bakinsa ya bushe, saboda haka ya aika a nemo masa alawar da ya saba amfani da ita, amma ba a samu ba.

Hon. Alasan Doguwa ya ce bayan da ba a samo alawar ba, sai aka kawo masa wani sabon samfurin “Ice mint” wanda ke sanya harshen mutum ya sauya launi zuwa shuɗi.

Ɗan majalisar ya zargi wasu mutane da ƙoƙarin bata masa suna a ciki da wajen Najeriya, yana mai cewa ba za su ci nasara ba.

Matakin da Alasan Doguwa zai ɗauka

A bayaninsa, ɗan majalisar ya bayyana cewa ba zai kai ƙarar waɗanda suka ɗauki hotonsa da nufin ɓata masa suna ga gwamnatin Kano ko rundunar ’yan sanda ba.

Alasan Ado Doguwa ya ƙara da cewa ba shi da niyyar zuwa kotu domin neman a bi masa hakkinsa, amma zai ɗauki mataki kan waɗanda suka yi yunƙurin bata masa suna.

Kara karanta wannan

Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River

A kalamansa:

“Ni bawa ne na Allah. Allah da nake bautawa bai muzanta ni ba, bai tozarta ni ba. Yau ɗin nan ina da niyyar tafiya aikin Hajjin bana. A matsayi na wanda Allah Ya yi alƙawarin zai karɓi addu’ar matafiyi, na miƙa wa Allah wannan al’amari.”
Hon. Alasan Ado Doguwa ya kuma yi Allah wadai tare da roƙon Allah Ya saka masa kan masu yunƙurin ɓata masa suna.

Rashin tsaro ya fusata Doguwa

A baya, mun wallafa cewa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya nemi daukar matakan gaggawa a majalisa saboda matsalar tsaro da ya ce ta yi tsanani, inda ya ce kashe-kashe, garkuwa da mutane da hare-hare sun kai kololuwa.

Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa lamuran tsaro sun kai wani mataki mai tayar da hankali, inda ya ce ya kamata ayyana dokar ta-baci a majalisa, a rufe ta baki daya domin kara fito da matsalar da ake fama da ita.

Ya jaddada cewa matsalar tsaro tana da tasiri kai tsaye a rayuwar jama’a — manoma, ’yan kasuwa, da masu ibada, kuma jama'a za su ci gaba da zama a cikin mawuyacin hali idan ba a dauki matakin da ya dace ba

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng