Pantami ko Jamilu Gwamna: An Ji Wanda Ya Fi Cancanta Ya Zama Ɗan Takarar APC a Gombe

Pantami ko Jamilu Gwamna: An Ji Wanda Ya Fi Cancanta Ya Zama Ɗan Takarar APC a Gombe

  • APC ta tabbatar da cewa za ta yi amfani da tsarin kato bayan kato wajen zaben fitar da gwani na gwamna a jihar Gombe bayan rikicin sulhu
  • Barista Isiyaku Danlawan ya ce mafi yawan masu neman takara sun amince da tsarin sulhu da ya fifita Dr. Jamilu Gwamna, in banda tsiraru
  • Danlawan ya bayyana cewa Sheikh Isa Pantami malami ne mai kima amma bai da tubalin siyasar da zai iya kai shi ga nasara a jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gombe - Yayin da APC ta shirya gudanar da zaben fitar da gwani na kujerun gwamnoni, kallo ya koma Gombe, inda za a fatata tsakanin Farfesa Isa Ali Pantami, Dr. Jamilu Isyaku Gwamna da wasu 'yan takara.

Barista Isiyaku Ahmed Danlawan, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Gombe, ya yi tsokaci game da zaben, da wanda yake ganin ya fi cancanta ya zama d'an takarar APC.

Kara karanta wannan

Jerin jihohin da APC za ta yi zaben fitar da gwani bayan gaza yin sasanci

Barista Isiyaku Danlawan ya yi magana game da zaben fitar da gwani na APC a jihar Gombe.
Dr. Jamilu Isyaku Gwamna, da Barista Isiyaku Danlawan, da Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Jamilu Isyaku Gwamna, Professor Isa Ali Pantami, Isiyaku Ahmed Danlawan
Source: Facebook

APC za ta yi kato bayan kato a Gombe

Tun da fari, jaridar Premium Times ta rahoto Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sanar da cewa APC za ta yi amfani da tsarin kato bayan kato don fitar da 'yan takara, bayan an gaza cimma matsaya a sulhu.

An samu wasu 'yan takara, irin su Isa Ali Pantami da suka ki amince wa da tsarin sulhu da masu ruwa da tsaki da gwamna suka yi amfani da shi don ayyana Dr. Jamilu Gwamna a matsayin d'an takara a Gombe.

"A makonnin da suka gabata, da goyon bayan kwamitin dattawan APC, da kwamitin gudanarwar jam'iyya na jihar, muka yi yunkurin amfani da tsarin sulhu don tsayar da 'yan takara, amma hakan ba ta cimma ruwa ba."

- Gwamna Inuwa Yahaya.

Gwamnan ya ce saboda turjiyar da wasu masu neman takara suka nuna, dole ta sanya, za a yi amfani da sashe na 87(2) na dokar zaben Najeriya don gudanar da zaben fitar da gwani a tsarin kato-bayan-kato a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Jami'in gwamnatin Tinubu ya goyi bayan takarar Pantami a Gombe

Wane hali siyasar Gombe take ciki?

A zantawar Legit Hausa da Barista Isiyaku Ahmed Danlawan, shugaban tafiyar MASS, ya yi magana game da zaben fitar da gwani da APC za ta gudanar a jihar Gombe.

Barista Danlawan ya ce:

"Abu na farko da za mu fara kallo shi ne, gwamna ya sanar da cewa shi da masu ruwa da tsaki, watau dattawa na APC, 'yan takara da shugabannin jam'iyya sun yi ittifaki, suka ga dacewar a ayyana Dr, Jamilu Gwamna a matsayin dan takara na sulhu.
"A cikin masu neman takara 11, an samu kusan masu neman takara tara da suka amince da matsayar shugabannin jam'iyyar. Amma saboda wasu ba su amince ba, sai gwamna ya yi amfani da dokar zabe don a magance wannan matsala, an yi komai dai dai da doka."

Pantami da kin amince wa da sulhu a Gombe

Game da yadda Farfesa Isa Ali Pantami ya nuna cewa ba zai amince da tsarin sulhu don tsayar da d'an takara a Gombe ba, Barista Danlawan ya ce:

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

"A zahirance, idan muka yi duba da masu neman takarar da suke da damar samun tikiti a APC, to Pantami ba zai wuce na shida ba, ba zai iya haura wa na biyar ba, saboda idan akwai wadanda ya kamata a ce sun fito sun soki tsarin sulhu, to wasu ne ya kamata ba wai shi Pantami ba.
"Ko a lokacin da aka fara zama kan batun sulhu, shi kansa ya fito ya fadi har kwanan watan zaman farko da aka yi, Gwamna Inuwa ya zauna da dukkan 'yan takara na mukamai daban daban, suka yi yarjejeniya, cewa za a yi amfani da sulhu a fitar da 'yan takara."

Barista Danlawan ya ce bayan wannan zaman, an ga yadda Pantami ya rika bin bayan gwamnan Gombe a duk inda yaje kaddamar da ayyuka, da tunanin cewa za a zabe shi matsayin dan takarar gwamna a APC.

Gwamna ya bi cancanta wajen zaben Jamilu Gwamna

Barista Isiyaku Danlawan ya ce gwamna ya zabi Dr. Jamilu Gwamna bisa cancanta a Gombe.
Dr. Jamil Isyaku Gwamna, wanda ke neman takara a Gombe da Barista Isiyaku Danlawan. Hoto: Hoto: Jamilu Isyaku Gwamna, Isiyaku Ahmed Danlawan
Source: Facebook

Sai dai, masanin shari'ar, ya yi zargin cewa, Pantami ya dawo daga baya ya kekashe kasa, ya ki amincewa da tsarin sulhu da ya fito da Dr. Jamilu gwamna a matsayin d'an takara, saboda an hana shi tikiti.

"Ya fito yana cewa gwamna ya zabi wanda yake so ne kawai ya ba shi tikiti, to maganar gaskiiya shi ne, da gwamna ya zabi wanda ya fi so ne, to ba Dr. Jamilu zai zaba ba, akwai yaransa da suka nemi takarar ai.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi fatali da buƙatar malaman addini, ya ƙi kashe masu kudin al'umma

"Akwai amininsa, Arc. Yunusa Yakubu, wanda suna tare tun tali tali, akwai kuma babban akawu, Malam Aminu Yusuf, yaronsa ne, akwai kuma Muhammad Gambo Magaji, kwamishinan kudi na Gombe; wadannan duk na hannun daman gwamna ne, ka ga da son ransa zai bi, to da a cikinsu ne zai fitar da dan takara.
"Amma saboda gwamna ya tuntubi manya na jam'iyya, duk inda ya je zai ji ana cewa Dr. Jamilu Isyaku Gwamna ne ya fi cancanta, saboda haka gwamna ya yi adalci, a matsayinsa na shugaba, ya amince da zabin jama'a, kuma ya yi abin da ya dace."

- Barista Isiyaku Ahmed Danlawan.

Pantami ko Jamilu Gwamna, wa ya fi cancanta?

Game da wanda ya fi cancantar zama d'an takarar APC a zaben gwamnan jihar Gombe, Barista Danlawan ya ce:

"A magana ta gaskiya, Pantami malami ne, wanda kuma kowa ya san shi a wannan fanni, amma shi ba dan siyasa ba ne, ba shi da wani tubali na siyasa da zai iya dogara da shi har ya samu tikiti.
"Kamar dai a ce jariri ne za a haifa yau, amma kuma gobe, ya ce a cika masa mota da fasinja ya tuka su, ko kuma a ce, mutum ne zai musulunta da la'asar, da magriba kuma ya ce zai ja mutane sallah, ka ga ai ba abu ne mai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Pantami ya bayyana muhimmancin zaben fitar da gwani ga jam'iyyar APC, ya yi gargadi

"Kowa ya san Pantami ne a fuskantar malanta, kuma ana girmama sa a kan hakan. Amma idan aka zo fagen siyasa, to ana maganar irinsu Dr. Jamilu Gwamna ne, wanda shi siyasar ma gadonta ya yi.
"A jam'iyyance ma, duniya ta gani lokacin da ya je sabunta shaidar zamansa dan APC, wani sakataren jam'iyya ya fito ya nuna cewa suna fushi da shi, saboda tun da ya tafi minista ya watsar da su.
"Amma shi Jamilu Gwamna, tun shekarun 1990 yake siyasar nan, yake hidimtawa jama'a, har dai aka kafa APC, yana hidimtawa jam'iyya, babu wanda zai yi musu a kan hakan, ka ga dole jam'iyya shi ta sani, shi za ta zaba."

A karshe, Barista Danlawan, ya yi kira ga masu kada kuri'a, da su duba wanda ya fi cancanta don zabensa a matsayin dan takarar gwamna na APC, kuma tafiyarsu ta MASS, watau tafiyar bunkasa siyasar Dr. Jamilu Isyaku Gwamna za ta ci gaba da sanya ido da wayar da kan jama'a game da siyasar cancanta a jihar Gombe.

APC ta kwantar da hankalin Pantami

A wani labari, mun ruwaito cewa, APC ta yi bayani kan matakin da ta dauka na fitar da 'yan takara ta hanyar masalaha a jihar Gombe yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Mai magana da yawun APC na jihar Gombe, Moses Kyari ya ce duk dan takarar da bai gamsu da tsarin sulhu ba, zai iya fitowa a yi zaben tsaida gwani.

Wannan na zuwa ne bayan tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami da Sanata Muhammed Danjuma Goje sun nuna ba su yarda ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com