Sanatocin APC Sun Jajubo Rigima da Jam'iyyar, an ba Su Wa'adi Su Gyara Alaka da Ita
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bai wa sanatocinta guda 2 wa’adin kwanaki 14 kan zargin cin dunduniyarta
- Hakan ya biyo bayan furucin sanatocin cewa Gwamna Alex Otti zai sake lashe zaben 2027, yayin da daya ya ce zai zabi gwamnan
- Jam’iyyar ta ce rashin neman gafara cikin wa’adin zai sa a kafa kwamitin ladabtarwa, wanda zai iya ba da shawarar hukunci kan ’yan majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Reshen jam’iyyar APC na Abia ya bai wa Sanata Orji Uzor Kalu da Chris Nkwonta kwanaki 14 su nemi gafara a bainar jama’a.
Jam’iyyar ta ce dole ne su nemi gafara kan kalaman da ta bayyana a matsayin waɗanda suka saba wa manufofin jam’iyyar, ko kuma su fuskanci matakin ladabtarwa.

Kara karanta wannan
ADC ta ji kamshin hadakar 'yan adawa, ana son tsayar da dan takara ya tunkari Tinubu

Source: Twitter
Musabbabin abin da ake zargin sanatocin
Kwamitin Aiki na Jiha (SWC), ƙarƙashin jagorancin shugaban APC na Abia, Chijioke Chukwu, ya yanke hukuncin yayin wani taro da aka gudanar a Umuahia, cewar The Nation.
Matakin ya biyo bayan kalaman Kalu a gidan talabijin na ƙasa cewa Gwamnan Abia, Alex Otti na Labour (LP), zai sake lashe zaɓen gwamna a 2027.
Haka kuma, Nkwonta ya bayyana a wani liyafar maraba da aka shirya wa matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a Ukwa East, cewa zai zaɓi Otti.
A cewar wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Uche Aguoru, ya fitar, SWC ta amince baki ɗaya cewa kalaman ’yan majalisar biyu ba su dace da matsayin ’yan siyasa ba.
Kwamitin ya ce kalaman sun jawo wa jam’iyyar kunya tare da yin illa ga haɗin kan APC da damar da take da ita ta lashe zaɓe a 2027.

Source: Facebook
Sanatoci 2 sun saba dokar APC a Najeriya
APC ta ce irin wannan hali ya saba wa sashe na 21.2(11) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ya ba ta damar ɗaukar matakin ladabtarwa kan mambobin da ayyukansu ke cutar da jam’iyyar.
Kwamitin ya buƙaci Sanata Kalu da Nkwonta su gabatar da cikakkiyar neman gafara a bainar jama’a cikin wa’adin kwanaki 14 da aka ba su.
Ta ce hakan zai nuna cewa suna da niyyar ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar tare da mara wa APC da ’yan takararta na 2027 baya, cewar Tribune.
Jam’iyyar ta yi gargadin cewa idan suka ƙi bin umarnin, za a kafa kwamitin ladabtarwa domin binciken lamarin da bayar da shawarar matakin da ya dace.
APC ta ƙara da cewa za a iya janye goyon bayan siyasa da wasu gata daga hannun ɗaya daga cikin ’yan majalisar idan aka tabbatar da cewa ayyukansa sun saba wa muradun jam’iyyar.
Fastoci: Sanata APC ya ce zai yi murabus
An ji cewa Sanata Orji Kalu daga jihar Abia ya bayyana abin da zai jawo ya fice daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Kalu ya ce kalaman masu taimaka wa shugaban ba lallai su wakilci ra'ayin Tinubu ba, yana jaddada cewa shugaban na da kyakkyawar alaka da Cocin Katolika.
Ya kuma amince cewa tattalin arzikin talakawa na cikin ƙalubale duk da ci gaban da gwamnati ta samu a bangaren manyan tsare-tsaren tattalin arziki.
Asali: Legit.ng
