Duk da Yana NDC, Kwankwaso Ya Tabo Batun Aiki Tare da Atiku, ADC kafin Zaben 2027

Duk da Yana NDC, Kwankwaso Ya Tabo Batun Aiki Tare da Atiku, ADC kafin Zaben 2027

  • Madugun tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci kan abubuwan da suka shafi siyasa gabanin zaben 2027
  • Kwankwaso ya bayyana cewa ficewarsa daga jam'iyyar ADC ba ta raunana karfin 'yan adawa ba kan shiga zaben 2027
  • Tsohon gwamnan na Kano ya kuma tabo batun yiwuwar yin aiki tare da Atiku Abubakar gabanin zabne shugaban kasa da ake tunkara

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa ficewarsa daga jam’iyyar ADC ta haifar da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyun adawa.

Kwankwaso ya bayyana cewa shi da Atiku Abubakar har yanzu za su iya yin aiki tare kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Kwankwaso ya yi magana kan yin aiki tare da Atiku
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da tashar Arise TV ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

2027: Yadda 'yar Kwankwaso ta shawo kan shi game da hada kai da Obi

Kwankwaso ya yi magana kan aiki da Atiku

Madugun na Kwankwasiyya ya mayar da martani kan damuwar da ake da ita na cewa komawarsa jam’iyyar NDC tare da Peter Obi ya raba kan ’yan adawa gida biyu gabanin zaɓen 2027.

“Yanzu haka, har yanzu za mu iya yin aiki tare kafin zaɓe. Ni kaina, kuma ina jin har shi kansa Obi, mun yanke shawarar barin ADC ba wai don muna faɗa da Atiku ba ne ko wani a can. Mun yanke shawarar barin wannan jam’iyyar ne saboda mun fahimci cewa akwai wasu matsaloli."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya ce akwai rikici a ADC

Ya bayyana cewa ADC na fama da wasu manyan matsaloli guda uku da ba a warware ba waɗanda ya yi amannar cewa za su wahalar da jam’iyyar wajen gabatar da ’yan takara, koda yake bai fito fili ya bayyana ko mene ne waɗannan matsalolin ba.

“Ko za su iya gabatar da ’yan takara a wannan jam’iyyar ko a’a, magana ce ta lokaci kawai. Ba wai mun yi zaɓen fitar da gwani ba ne."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya haska dalilin Arewa na aiki da Peter Obi don zaben 2027

- Rabiu Musa Kwankwaso

Waɗannan kalamai na zuwa ne bayan da Atiku ya yi iƙirarin cewa shaharar Kwankwaso ta taƙaita ne a jihar Kano kaɗai, sannan kuma Gwamna Abba Yusuf ya ƙara raba kan mabiya a can.

Kwankwaso ya koma jam'iyyar NDC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya tuna baya kan Atiku

Kwankwaso ya kuma tuna da tarihin yin aiki tare da Atiku, inda ya tunatar da cewa ya yi aiki a matsayin mai kula da yankin Arewa na tsohon mataimakin shugaban ƙasar a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2019.

“An yi zaɓe a 2019 a Port Harcourt. Shi ya yi nasara a zaɓen. Na kasance mai taya shi gudanar da aiki a arewa. Mun yi masa aiki."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Ya nuna asalin dangantakarsa da Atiku tun daga zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na APC da aka yi a Legas a 2015, inda ya zo na biyu bayan Muhammadu Buhari, yayin da Atiku ya zo na uku.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hakura, ya shirya goyon bayan Peter Obi ko wani 'dan takara a zaben 2027

Kwankwaso ya magantu kan Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan yin aiki tare da Peter Obi.

Kwankwaso ya bayyana cewa shugabannin siyasar Arewa sun amince da Peter Obi, a matsayin mafi cancanta don fuskantar babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya yi watsi da damuwar da ake nunawa game da wani boyayyen rikicin neman iko tsakanin sansaninsa da na Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng