Kafin Komawa NDC, Kwankwaso da Peter Obi Sun Yi Yunkurin Shiga Jam'iyyar PRP
- Jam'iyyar PRP ta yi ikirarin cewa tsofaffin yan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso sun nemi shiga jam’iyyar
- A cewar PRP, bukatun da manyan jiga-jigan biyu suka bijiro da su ciki har da tikitin takara ne suka sa ta ki amincewa
- Shugaban jam'iyyar na kasa, Dr Hakeem Baba Ahmed ya ce PRP ba za ta taba karya dokokinta saboda bukatun wani ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban PRP na kasa, Dr Hakeem Baba Ahmed, ya ce tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, sun yi yunkurin shiga jam'iyyarsu.
A cewarsa, manyan jagororin adawar biyu sun tattauna da PRP domin duba yiwuwar shiga cikin jam'iyyar, amma daga karshe ba a samu matsaya ba.

Source: UGC
Daily Trust ta ruwaito cewa a wata hira da aka yi da shi, Baba Ahmed ya ce tattaunawar da aka yi tsakanin PRP da jiga-jigan ta tsaya ne saboda wasu sharuddam da suka gabatar kafin shiga jam’iyyar.
Abin da Kwankwaso da Obi suka nema
A cewarsa, Obi da Kwankwaso sun tuntubi PRP domin yiwuwar hadin gwiwa, kuma har an kai matakin kafa kwamitin ci gaba da tattaunawa.
“Sun zo suka ce suna son shiga PRP, amma lokacin da muka zauna muka tattauna da su, sun gabatar da wasu bukatu.
“Kafin su shiga, sun nemi q ba su tikitin takarar shugaban kasa, ma’ana dole a ba su tikitin. Muka ce a’a, wannan PRP ce; ba ma irin wannan siyasar,” in ji Baba Ahmed.
Sharadin da PRP ta gidaya masu
Ya bayyana cewa jam’iyyar ta dage cewa dole Obi da Kwankwaso su fara shiga PRP a hukumance sannan su bi tsarin jam’iyyar kafin neman kowace kujera.
“Na gaya musu cewa ku fara shiga jam’iyya. Bayan kun shiga sai ku ce ni Obi ne ina son tsayawa takarar shugaban kasa, ko ni Kwankwaso ne ina son zama mataimakinsa.
“Amma ku zo tun kafin a yanke hukunci kuna neman a tabbatar muku da tikiti ba tare da hamayya ba, idan da gaske kuna da karfi me ya sa kuke tsoron a fita a gwabza?” ya tambaya.
Baba Ahmed ya ce shugabannin PRP sun san irin tasirin siyasar Obi da Kwankwaso, amma ba za su karya kundin tsarin jam’iyya saboda su ba.
“Mun san idan mutum ya ga Obi da Kwankwaso tare zai ce manyan ‘yan takara sun iso, to mma ba za mu karya dokokin jam’iyyarmu ba,” in ji shi.
NDC ta tsaida kudin dam din takara
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta NDC ta fitar da kudin fom domin masu son shiga takara a matakai daban-daban gabannin zaben 2027.
Hakan na zuwa ne bayan gudanar da babban taron jam'iyya na kasa a makon da ya wuce, wanda ya samu halartar Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.
NDC ta sanya kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙasa a kan Naira miliyan 60, wanda ya ƙunshi Naira miliyan 20 na fom ɗin nuna sha’awa da kuma Naira miliyan 40 na fom ɗin tsayawa takara.
Asali: Legit.ng

