Kano Ta Ware N300m na Auren Gata, an Fadi Yadda Kowace Amarya Za Ta Samu

Kano Ta Ware N300m na Auren Gata, an Fadi Yadda Kowace Amarya Za Ta Samu

  1. Gwamnatin Kano ta amince da fitar da Naira miliyan 300 domin tallafa wa shirin auren gata da Hukumar Hisbah ke gudanarwa
  2. Kowace amarya za ta samu Naira 200,000 a matsayin jari da sadaki, yayin da sabbin ma’aurata za su samu kayan daki
  3. Shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ya bukaci ma’auratan su mutunta juna, tare da kai duk wata matsalar aure hukumar domin sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnatin Kano ta amince da fitar da miliyoyin Naira ga hukumar Hisbah a jihar domin sake auren gata kamar yadda aka saba.

Gwamantin jihar ta ware Naira miliyan 300 domin tallafa wa wadanda suka amfana da shirin aurar da mata da maza na Hukumar Hisbah.

Hisbah za ta sake auren gata a Kano
Shugaban hukumar Hisbah a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Source: Facebook

Shugaban Hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan yayin wani shirin wayar da kan ma’auratan da aka gudanar a Kano.

Kara karanta wannan

An sanya lokacin bikin auren gata, Gwamna Abba ya yi nasiha ga ma'aurata 1,500

Yawan kudin da za a ba kowace amarya

Ya ce kowace amarya za ta samu Naira 200,000 da za a saka kai tsaye cikin asusun bankinta, domin sadaki da kuma fara sana’a.

Daurawa ya kuma bayyana cewa gwamnatin Kano za ta samar da cikakkun kayan daki ga kowanne sabon ma’auraci, domin taimaka musu wajen fara rayuwar aure.

Ya kara da cewa kowane ango zai samu yadudduka guda 10, hula, takalma da kayan abinci, bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

An shirya gudanar da babban liyafar aure ranar Asabar a Gidan Gwamnati da ke Kano, inda manyan malaman Musulunci daga sassan Najeriya za su halarta domin yi wa ma’auratan addu’a.

Shugaban Hisbah ya shawarci ango da su rika kyautatawa matansu, girmama su da kuma sauke nauyin da ke kansu domin samar da zaman lafiya a gidajensu.

Haka kuma, ya bukaci amaren da su kasance masu hakuri da taimaka wa mazajensu, domin samun zaman aure mai cike da fahimtar juna.

Kara karanta wannan

Kano za ta karbi manyan baki, akwai babban taro a kan miyagun kwayoyi

Daurawa ya ce Hukumar Hisbah ba ta goyon bayan sakin aure ba tare da an yi kokarin sasanta rikicin da ya haifar da matsalar ba.

Ya bukaci ma’auratan da suka samu tallafi a shirye-shiryen aurar da ma’aurata na baya su halarci liyafar da za a gudanar ranar Asabar 8 ga watan Agustan shekarar 2026.

Wannan ba shi ne karon farko da hukumar ke jagorantar auren gata ba wanda gwamnatin jihar ke ba ta goyon baya a Kano domin ba masu son yi aure dama saboda dakile yawan badala a tsakanin mutane.

Hisbah ta kawo doka ga direbobin NAPEP

An ji cewa Hukumar Hisbah ta Kano ta haramta tsarin daukar mata da direbobin adaidaita sahu ke tana mai cewa ya saɓa wa koyarwar Musulunci.

Hisbah ta sanar da umarnin ne yayin ganawa da shugabannin BOTORA, inda suka tattauna hanyoyin inganta tsari.

Ta kuma buƙaci haɗin kai wajen yaƙi da satar yara, fataucin miyagun ƙwayoyi da rashin ɗa’a, yayin da BOTORA ta yi alƙawarin bin umarnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.