An Tono Wata Doka, Tinubu na Iya Rasa Damar Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

An Tono Wata Doka, Tinubu na Iya Rasa Damar Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

  • Jam'iyyar adawa ta ADC ta yi ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba
  • Lauyan jam'iyyar ADC, Kalu Kalu, ya zargi shugaban kasa da gabatar da takardun bogi ga hukumar zabe ta kasa watau INEC
  • Kalu ya kafa hujja da Sashe na 137(1)(j) na kundin tsarin mulkin Najeriya, yana mai cewa doka ta haramtawa Tinubu takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba.

ADC ta danganta hakan da zargin rashin gabatar da takardun karatunsa na firamare da sakandare ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jagorantar taron FEC a fadar shugaban kasa da ke Abuja Hoto: @OfficiaABAT
Source: Twitter

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa a cikin fom din takarar da aka mika wa INEC, Tinubu ya bar guraben da suka shafi bayanan karatunsa na firamare da sakandare babu komai, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sun gano matsalar da za ta kawo cikas ga Tinubu a 2027

ADC ta yi zargin gabatar da takardun bogi

Da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels tv, lauya kuma jigo a ADC, Kalu Kalu, ya yi zargin cewa shugaban kasar ya aikata laifin gabatar da takardun bogi, abin da ya ce zai iya hana shi cancantar tsayawa takara.

Kalu ya kafa hujja da Sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda ya ce ya haramta wa duk wanda ya gabatar da takardar bogi ga INEC tsayawa takarar shugaban kasa.

Ya yi magana kan makarantun Tinubu

A cewar Kalu, makarantun firamare da sakandaren da Tinubu ya ce ya halarta ba su wanzu a lokacin da ya bayyana ko kuma an gabatar da bayanansu ba daidai ba.

Ya kuma yi ikirarin cewa binciken da Atiku Abubakar ya gudanar bayan zaben 2023 ya sa shugaban kasar bai sake bayyana bayanan karatunsa na firamare da sakandare a sabon fom din da ya mika wa INEC ba.

Kara karanta wannan

Yan Arewa sun taso Kiristoci a gaba kan Tinubu, sun sha alwashi kan zaben 2027

Ya tabo batun takardar jami'ar Chicago

Jigon na ADC ya kuma yi tambaya kan sahihancin takardar shaidar karatun digirin Tinubu daga Jami'ar Chicago da ke Amurka, yana mai cewa an taba bincikenta a wata kotu da ke Amurka.

Kalu ya ce:

"Atiku Abubakar ya nemi a bayyana bayanan karatun Bola Ahmed Tinubu, kuma kotun Amurka ta umurci jami'ar Chicago ta fitar da su."
Tutar ADC.
Tutar jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya Hoto: @BlolajiADC
Source: Twitter

Ya kara da cewa bayanan da aka fitar sun nuna cewa Tinubu ya yi ikirarin ya kammala karatu a Government College, Lagos a shekarar 1970, alhali makarantar ta fara aiki ne a shekarar 1974.

A cewarsa, idan kundin tsarin mulki ya haramta wa wanda ya gabatar da takardar bogi tsayawa takara, to wannan tanadi ya fi karfin duk wata doka da za ta saba masa.

Malami ya hango matsala ga Tinubu

Kun ji cewa Primate Elijah Ayodele ya ce wasu daga cikin mutanen da shugaban kasa Bola Tinubu ya dogara da su za su ba shi kunya a zaben 2027.

Malamin addinin ya yi ikirarin cewa an rufe wa Tinubu ido ta fuskar ruhi, yayin da wasu gwamnonin da yake dogara da su ba za su iya lashe jihohinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262