An Kashe Dan Siyasa da 'Yan Bindiga Suka kai Kazamin Hari Filato da Dare
- Tsohon kansilan mazabar Rim a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau, Daniel Danjuma Chong, ya rasu bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai masa
- Maharan sun kuma harbe wani mazaunin yankin mai suna David Danjuma, wanda ke ci gaba da karɓar magani sakamakon raunukan harbin bindiga
- Ƙungiyar matasan Berom ta yi Allah wadai da harin, tare da buƙatar jami'an tsaro su kamo waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jos – Wasu 'yan bindiga sun kashe tsohon kansilan mazabar Rim da ke ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau, Daniel Danjuma Chong, wanda aka fi sani da "Hon. Star."
An ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:45 na daren Lahadi a ƙauyen Torok da ke yankin Rim, inda maharan suka buɗe wuta kan mazauna yankin kafin su tsere.

Source: Original
Punch ta rahoto cewa harin ya jefa al'ummar yankin cikin firgici, yayin da mutane suka rika gudu domin tsira bayan jin ƙarar harbe-harbe.
Yadda aka kai hari Filato
Wata mazauniyar yankin mai suna Cynitha Dung ta ce sun ji karar harbe-harbe masu ƙarfi a cikin dare, lamarin da ya tilasta wa jama'a neman mafaka.
Ta ce bayan harin ne aka gano cewa an harbe tsohon kansilan har lahira.
A cewarta:
"Mun ji harbe-harbe masu yawa da daddare. Kowa ya gudu domin tsira. Da mutane suka fito daga baya, sai aka tarar an harbi Hon. Daniel. Abin ya tayar mana da hankali sosai."
Ta kuma bayyana cewa wani mazaunin yankin mai suna David Danjuma ya samu raunukan harbin bindiga kuma yana karɓar magani.
Kiran kungiyar Berom a Filato
Vanguard ta wallafa cewa kungiyar Berom ta BYM ta yi Allah wadai da kisan, tana mai bayyana shi a matsayin wani sabon hari kan al'ummar ƙaramar hukumar Riyom.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Rwang Tengwong, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta buƙaci jami'an tsaro da gwamnatin jihar Plateau su gaggauta kamo waɗanda suka kai harin.

Source: Twitter
Har ila yau, ƙungiyar ta yi kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke fama da hare-hare, tare da rusa maboyar masu aikata laifuffuka da kuma ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen kashe-kashen fararen hula.
An ce ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Plateau, SP Alfred Alabo, bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
An ceto babban jami'in soja a Enugu
A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun ceto babban jami'in soja, Laftanar Kanal Ofor Amobi, da wani farar hula bayan shafe kwanaki 10 suna gudanar da samame a jihar Enugu.
Rahoton rundunar sojin ya bayyana cewa an ceto mutanen ne sakamakon matsin lamba da dakaru suka ci gaba da yi wa masu garkuwar.
Aikin ceton ya samu haɗin gwiwar dakarun rundunar soji, rundunar ruwa da kuma rundunar musamman ta sojoji a ƙarƙashin Operation UDO KA.
Asali: Legit.ng

