Ana Fargabar Harin Sojojin Sama Ya Kashe kusan Mutane 100 a Zamfara
- Rahotanni sun nuna an samu asarar rayuka a jihar Zamfara sakamakon harin da sojoji suka kai kan 'yan bindiga
- Majiyoyi sun bayyana cewa harin wanda ya sauka a wata kasuwa ya jawo asarar rayukan fararen hula tare da raunata wasu da dama
- Kungiyar Amnesty ta kiyasta cewa an hallaka wajen mutum 100 inda a kauye daya kawai aka binne mutane 80 a lokaci guda
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Aƙalla mutane 72 ne aka ruwaito cewa an kashe bayan da wani harin sama na dakarun sojoji a jihar Zamfara.
Harin sojojin ya faɗa kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2026.

Source: Facebook
Tashar France24 ta ce kamfanin dillacin labarai na AFP ya tabbatar da harin na dakarun sojoji wanda ya jawo asarar rayuka a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP
Ana zargjn sojoji sun kashe farar hula
Wani jagoran al'umma, Garba Ibrahim Mashema, ya bayyana cewa gawarwakin wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa "sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba".
"Yawan mutanen da suka mutu yana da wuyar tabbatarwa a halin yanzu. Kowa, mazauna gari da 'yan bindiga duk suna zuwa kasuwar. Mutane suna ƙarƙashin ikon 'yan bindiga ne. Babu abin da za su iya yi."
- Garba Ibrahim Mashema
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa 'yan bindiga ne ke iko da kasuwar Tumfa, kuma wasu daga cikin waɗanda aka kashe "ƙananan 'yan mata ne masu sayar da fura da waina a kasuwar".
Amnesty ta fadi mutanen da aka kashe
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta bayyana a shafinta na X cewa adadin waɗanda suka mutu ya haura mutane 100.
Ta ƙara da cewa mutane da dama waɗanda suka ji rauni suna karɓar magani biyo bayan harin wanda aka kai ta sama.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari
Ƙungiyar ta ce a ɗaya daga cikin ƙauyukan da abin ya shafa an binne mutane 80 a lokaci guda.
"Dole ne hukumomi su gudanar da bincike kan waɗannan hare-hare masu kisa, sannan su dakatar da hare-haren sakaci kan farar hula."
“A sassan arewa da ke fuskantar rikici, farar hula ne suka fi fuskantar wahala akai-akai. Bai kamata a yi watsi da waɗannan munanan mace-mace ba. Waɗanda suka tsira a cikin mawuyacin hali da iyalansu sun cancanci sanin gaskiya, adalci, da kuma biyan diyya."
“Jiragen yaƙin soja sun yi luguden boma-bomai a kasuwar mako-mako, a daidai lokacin da take cike da mutane kuma ba tare da wani gargaɗi ba."
“An yi ta kururuwa, jini, da gawarwaki a ko'ina a ƙasa. Waɗanda suka tsira da raunuka an kwashe su zuwa manyan asibitoci a Zurmi da Shinkafa, yayin da waɗanda suka ji rauni sosai suke karɓar magani a asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau.”

Source: Original
Sojoji sun musanta kashe farar hula
Harba makamin na Zamfara ya faru ne a rana ɗaya da wani aikin rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) da ya nufi 'yan bindiga a jihar Neja, ya kashe farar hula 13.
Michael Onoja, mai magana da yawun hedikwatar tsaro, ya bayyana cewa rahotannin asarar rayukan farar hula a Zamfara "ba gaskiya ba ne".
Sojojin sun kuma musanta rahotannin cewa an kashe farar hula a harin sama na jihar Neja, kodayake sun ce za a gudanar da bincike kan lamarin.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma sun karkashe ’yan ta’adda da dama a jihar Zamfara.
Sojojin sun hallaka tsagerun ne yayin wani harin sama da aka kai a wurin taron jagororin ’yan ta’adda a jihar Zamfara.
Rahotannin sirri sun tabbatar da cewa ’yan ta’addan sun taru ne a wani boyayyen wuri a ƙauyen Tumfa da ke ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng
