Wike Zai Hana Sana'ar Acaba da Masu Adaidaita Sahu Aiki a Birnin Abuja

Wike Zai Hana Sana'ar Acaba da Masu Adaidaita Sahu Aiki a Birnin Abuja

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana damuwa game da yawaitar ayyukan ta'addanci a birnin Abuja
  • Wike ya bayyana cewa rahotannin jami'an tsaro sun nuna masu laifi na amfani da babura wajen aikata laifuka, saboda haka ana shirin ware wuraren hana su
  • Ministan ya kuma ce an amince da kayan tallafin tsaro, yayin da ya ce matsalar mabarata na ci gaba saboda suna komawa Abuja bayan an mayar da su jihohinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa suna ƙoƙarin daukar matakai kan ayyukan ta'addanci a birnin.

Wike ya bayyana cewa gwamnatin Abuja na nazarin yiwuwar haramta zirga-zirgar baburan haya, da aka fi sani da okada, da kuma adaidaita sahu a wasu sassan Abuja saboda karuwar matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Faston da ya buga da Tinubu a fadar shugaban kasa ya sake magana

Wike ya duba yiwuwar hana zirga-zirgar babu da adaidaita sahu a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike yana jawabi ga manema labarai. Hoto: @Olayinkalere.
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da manema labarai na wata-wata, wanda aka watsa kai tsaye a tashar Channels TV ranar Talata.

Abuja: Rahotannin sirri da hukumomi ke samu

Wike ya ce an dauki wannan mataki ne bayan Majalisar Tsaron Babban Birnin Tarayya ta ba da shawara sakamakon rahotannin sirri da suka danganta amfani da babura da ayyukan masu laifi.

Ministan ya ce ya amince da wasu sabbin matakan karfafa kayan aikin jami'an tsaro, tare da umartar hukumomin tsaro su tantance wuraren da ya dace a hana zirga-zirgar okada da adaidaita sahu.

Wike ya ce:

"Baya ga haka, kamar yadda kuka sani, da safiyar yau na sanya hannu kan amincewa bayan taron Majalisar Tsaro, inda muka yanke shawarar cewa baya ga kasancewarsu abin takura, sun zama barazana ga tsaro.

Ya kara da cewa:

"Rahotannin jami'an tsaro sun nuna cewa idan 'yan bindiga za su fita aikata laifi, suna amfani da babura."

Kara karanta wannan

Wike zai rusa 'ruga' da aka samar babu ka'ida a Abuja, ya fadi illarsu ga al'umma

Wike ya fadi matakan da suke ɗauka kan yawan aikata laifuffuka a Abuja
Tsohon gwamnan Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: @Olayinkalere.
Source: Twitter

Tuntuntuni da Wike ke yi kan matakin

Sai dai ministan ya ce ba zai kasance mai sauki a haramta amfani da acaba da adaidaita sahu a duk fadin Abuja ba saboda girman birnin da kuma bukatun sufuri na mazauna yankin.

Ya ce ya umarci jami'an tsaro su tsara wuraren da ba za a bukaci okada da adaidaita sahu ba, musamman a tsakiyar birnin Abuja, inda ake ganin ya dace a hana zirga-zirgarsu.

Wike ya kuma bayyana cewa ya amince da fitar da kayan tallafi da dabarun aiki domin taimaka wa jami'an tsaro wajen aiwatar da sabon shirin.

Da yake magana kan yawaitar mabarata a babban birnin kasar, Wike ya ce kokarin kwashe su daga tituna yana ba da sakamako na dan lokaci ne kawai, domin suna dawowa bayan an mayar da su.

Ya ce:

"Mabarata na ci gaba da cika ko'ina. Duk lokacin da muka kwashe su muka mayar da su, bayan wani lokaci sai su sake dawowa."

Kara karanta wannan

Yadda malaman addinin Kirista suka kai ruwa rana da Tinubu a Aso Villa

Wike ya fadi sharadin barin ofis

An ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙalubalanci duk mai musanta nasarorin gwamnatinsa kan titunan ƙauyukan birnin tarayya ya fito cikin sa'o'i 48.

Wike ya ce gwamnatin Abuja ta ba da kwangilar kilomita 317 na tituna, ta kammala kilomita 221, yayin da ake ci gaba da aikin kilomita 96 .

Ministan na Abuja ya bayyana cewa zai yi murabus idan aka tabbatar da cewa bayanan da ya bayar ba gaskiya ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.