Babban Malamin Addini Ya Yi Gyara kan Batun Tinubu zai Fadi Zaben 2027
- Primate Elijah Ayodele da ake zargin ya yi hasashen Bola Tinubu zai sha kasa a zaben 2027 mai zuwa ya ce ba a fahimci kalamansa ba sam
- Ya zargi wasu 'yan siyasa da kafafen yada labarai da karkatar da bayanansa da ya yi a kan batun zaben da ke tafe kamar yadda ya saba
- Primate Elijah Ayodele ya ce idan lokaci ya yi ne kawai zai bayar da tabbaci a kan wanda zai lashe zaben shugaban kasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai samu wa'adin mulki na biyu ba a zaben shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu, Ayodele ya ce an karkatar da abin da ya fada domin amfanin wasu 'yan siyasa.

Source: Twitter
The Nation ta kawo labarin cewa Malamin ya bayyana cewa abin da ya fada ya fito ne a wani bidiyo da aka dauka yayin ibadar ranar Lahadi a cocinsa, inda ya ce bai taba cewa Tinubu zai sha kaye a zaben 2027 ba.
Fasto ya yi magana kan Tinubu
Daily Post ta ruwaito cewa Ayodele ya ce ya ga rahotanni da dama da ke danganta masa wannan furuci, amma ya jaddada cewa babu inda ya taba fadin cewa Shugaba Tinubu zai rasa damar sake lashe zabe.
A cewarsa, abin da ya fada shi ne:
"Idan Tinubu ya fadi zaben, hakan zai yi masa zafi."
Ya ce karkatar da wahayinsa ya zama tamkar al'ada ga wasu 'yan siyasa da wasu kafafen yada labarai domin cimma muradunsu, yana mai cewa wannan sabon lamari ya kara tabbatar masa da cewa ana yin hakan ne da gangan.
Fasto zai fadi wanda zai ci zabe
Malamin ya kara da cewa har yanzu bai kai lokacin da zai bayyana wanda zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 ba, yana mai cewa idan lokacin ya yi zai sanar da hakan.

Source: Facebook
Haka kuma ya bukaci kafafen yada labarai su rika tuntubar ofishinsa na yada labarai idan akwai bukatar karin haske kan duk wani bayani da ya fitar, maimakon wallafa rahotannin da ba su dace ba.
A cewarsa, yada bayanan da bai fada ba ba aikin jarida ne na kwarewa ba, yana kuma kira ga dukkan kafafen yada labarai su mutunta ka'idojin aikin jarida tare da tabbatar da gaskiya kafin wallafa labarai.
Tinubu na cikin tsaka mai wuya
A wani labarin, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan shirye-shiryen zaben shekarar 2027 musamman yayin da siyasa ke kara daukar zafi.
Primate Ayodele ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin tsaka mai wuya kan batun yin takara tare da Kashim Shettima a lokacin da ake ci gaba da adawa da batun Muslim-Muslim.
Ayodele ya ƙara da cewa Tinubu na iya fuskantar matsin lamba daga abokan siyasa da masu ba shi shawara, waɗanda za su iya tura shi ga ɗaukar wannan tsauraran mataki kan kujerar mataimakin shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng

