Kwankwaso Ya Hakura, Ya Shirya Goyon Bayan Peter Obi ko Wani 'Dan Takara a Zaben 2027

Kwankwaso Ya Hakura, Ya Shirya Goyon Bayan Peter Obi ko Wani 'Dan Takara a Zaben 2027

  • Tsohon 'dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce zai goyi bayan duk wanda NDC ta tsayar takara a zaben 2027
  • Hakan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta amince da mika tikitin shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya na wa’adi daya
  • Kwankwaso ya ce yana iya zama mataimakin 'dan takarar da NDC za ta dauko daga Kudu idan jam’iyya ta yanke shawarar hakan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa a shirye yake ya mara wa duk dan takarar da jam’iyyar NDC ta tsayar baya a zaben 2027.

Kwankwaso ya yi wannan furuci ne kwanaki kadam bayan ya koma NDC tare da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

Kwankwaso RM.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin PrimeTime na gidan talabijin na Arise TV.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Kwankwaso zai yi takara a 2027?

Jagoran Kwankwasiyya ya ce NDC ta cimma matsayar mika takara yankin Kudu ne bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki daga sassan kasar nan.

“Idan jam’iyya ta yanke shawarar in zama abokin takarar wani daga Kudu, a shirye nake na amince da hakan."
“Tun daga farko mun zauna muka duba halin da kasar nan ke ciki, sannan muka dauki manyan matakai ciki har da mika tikitin shugaban kasa zuwa Kudu na shekaru hudu, bayan haka mulkin zai dawo Arewa.”

Dalilin mika tikitin takara zuwa Kudu

Kwankwaso ya ce ‘yan Arewa da suka shiga jam’iyyar NDC sun amince da tsarin ne saboda suna ganin hakan zai taimaka wajen kawo karshen rikicin tsarin karba-karba, wanda ya biyo bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua.

“Muna ganin mafi dacewa shi ne a kai mulkin zuwa Kudu domin kawo karshen rudanin da ya biyo bayan rasuwar shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua.

Kara karanta wannan

SDP 2027: Jam'iyyar adawa ta farko ta tsaida ɗan takarar shugaban kasa

“Abin da ya fi muhimmanci yanzu ba Arewa ko Kudu ba ne, illa samun shugabanci nagari daga mutane masu himma da kishin kawo cigaba ga kasa,” in ji shi.
Tuyar NDC.
Sabuwar jam'iyyar adawa, NDC da hukumar INEC ta amince da kirkiro ta a Najeriya Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Kwankwaso da Obi sun tattauna kan tsaro

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa shi da Peter Obi sun tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro musamman a Arewacin Najeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

“Ni da Peter Obi mun tattauna hanyoyi da dama na yaki da rashin tsaro. Na yi aiki tare da mutane daga kowane bangare kuma na san ina da kwarewar da za ta taimaka,” ya ce.

Dalilin Kwankwaso na ficewa daga ADC

A baya, an ji cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce matsalolin da suka jawo ficewarsa daga ADC kusan iri daya ne da wanda ya jawo ya bar NNPP.

Ya bayyana hakan ne kwanaki bayan sauya shekarsa daga haɗakar yan adawa, ADC zuwa sabuwar tafiya ta NDC wadda ke ci gaba da jan hankali a siyasar Najeriya.

Kwankwaso ya ce sun gano cewa an shiga wani yanayi da ake ƙoƙarin durkusar da rajistar jam’iyyar ADC ta hanyar shari’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262