Kwankwaso Ya Sadaukar da Takararsa, Ya Goyi bayan NDC da Ta Mika Tikiti Kudu

Kwankwaso Ya Sadaukar da Takararsa, Ya Goyi bayan NDC da Ta Mika Tikiti Kudu

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya goyi bayan matakin jam’iyyar NDC na bai wa Kudancin Najeriya tikitin takarar shugaban ƙasa
  • Kwankwaso ya ce duk da an hana shi damar neman tikitin shugaban ƙasa, zai mutunta matsayar jam’iyyar tare da aiki domin haɗin kai
  • Kwararren 'dan siyasar ya bayyana cewa tsarin rabon tikiti tsakanin Arewa da Kudu zai taimaka wajen samar da haɗin kai da rage bambance-bambance

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rabiu Kwankwaso, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya yi magana kan matsayar jam'iyyar NDC kan tikitin shugaban kasa.

Rabiu Kwankwaso ya nuna goyon bayansa ga matakin jam’iyyar na bai wa Kudancin Najeriya tikitin takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Kwankwaso ya goyi bayan matakin NDC kan tikitin takarar shugaban kasa
Jigon NDC, Peter Obi, jagoran jam'iyyar, Seriake Dickson da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

Tikitin takara: Kwankwaso ya magantu kan matsayar NDC

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar a babban taron ƙasa da aka gudanar a Abuja ranar Asabar, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya san makomarsa da NDC ta yi matsaya kan tikitin takara

Ya ce matakin zai bai wa yankin Kudu damar kammala wa’adinsa na jagorancin ƙasa cikin tsarin karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu.

Kwankwaso, wanda tun farko ya nuna sha’awar neman tikitin shugaban ƙasa a jam’iyyar, ya ce duk da matakin ya hana shi damar tsayawa takara, zai mutunta matsayar jam’iyyar.

A cewarsa:

“Cikin haɗin kai da biyayya ga jam’iyya, ina goyon bayan bai wa Kudancin Najeriya tikitin shugaban ƙasa domin yankin ya kammala wa’adinsa na shugabancin ƙasa.”
Kwankwaso ya goyi bayan matsayar NDC kan takarar shugaban kasa
Sanata Rabiu Musa Kwanwkaso da Peter Obi yayin taro a Abuja. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

Kwankwaso ya fadi taimakon da tsarin zai yi

Tsohon ministan tsaron ya ce tsarin rabon tikiti zai taimaka wajen samar da haɗin kai da warkar da matsalolin siyasa da suka addabi Najeriya.

Ya kuma tabbatar da cewa mabiyansa da tsarin siyasar Kwankwasiyya za su yi aiki da umarnin jam’iyyar domin tabbatar da adalci da daidaito.

Kwankwaso ya ƙara da cewa jam’iyyar NDC za ta fifita shugabanci mai adalci ba tare da nuna bambancin ƙabila ko addini ba.

'Abin da NDC ta shirya yi wa Najeriya'

Ya ce jam’iyyar na son dawo da martabar Najeriya tare da tabbatar da mutunta ’yan ƙasa a gida da ƙasashen waje, kamar yadda Punch ta ce.

Kara karanta wannan

Yaron Atiku Abubakar ya sayi fam a ADC, zai nemi takarar sanata a Adamawa

Rahotanni sun nuna cewa bayan bai wa Kudu tikitin shugaban ƙasa, damar Peter Obi ta samun tikitin NDC ta ƙaru sosai gabanin zaɓen 2027.

Kwankwaso ya shiga jam’iyyar NDC ne bayan ficewarsa daga ADC, inda yake neman damar sake fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa a 2027 da ake tunkara nan gaba kadan.

Kwankwaso ya tabo batun Dadiyata

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci a tabbatar da adalci kan ɓacewar Abubakar Idris Dadiyata.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya yabawa sabon binciken da sufeton ‘yan sanda ya bayar da umarni a yi kan lamarin da ya dawo danye.

Sanata Kwankwaso ya nemi gwamnati ta tallafa wa Dadiyata da iyalansa idan bincike ya tabbatar yana raye, sannan a bi masa hakkinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.