2027: Yadda 'Yar Kwankwaso Ta Shawo kan Shi game da Hada Kai da Obi
- Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi karin bayani kan dalilin hadewa da tsohn dan takarar shugaban kasa, Peter Obi
- Kwankwaso ya bayyana cewa tun a zaben 2023 da ya gabata 'yar sa ta fara ba shi shawara ya hade da Peter Obi domin cimma nasara
- Hakan na zuwa ne bayan Rabiu Kwankwaso ya koma NDC tare da Obi, kuma ya amince da cewa dan Kudu ne zai yi wa jam'iyyar takarar 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa ’yar sa ta roƙe shi ya haɗa kai da Peter Obi tun a lokacin babban zaɓen shekarar 2023.
Hakan ya faru ne shekaru kafin daga baya manyan 'yan siyasar biyu su haɗa kai ƙarƙashin jam’iyyar NDC domin tunkarar siyasar 2027.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya hakura, ya shirya goyon bayan Peter Obi ko wani 'dan takara a zaben 2027

Source: Facebook
Abin da 'yar Kwankwaso ta ce
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Arise TV ranar Litinin, inda ya yi amfani da labarin wajen nuna muhimmancin hadin kai a siyasa.
“Har ma a zaɓen 2023, a gidana, ’yata ce take gaya min na je na yi aiki tare da Peter Obi. Ba ta ce ita ’yar Obidient ba ce, amma tana son mu yi aiki tare da shi,”
In ji shi.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi magana yana nuna cewa tasirin tafiyar Kwankwasiyya da kuma magoya bayan Obi ya fi yadda masu sharhin siyasa suke zato zurfi a yankuna daban-daban.
“Za ka yi mamaki, har ma a gidanka ko gidan kowa a Kudu, akwai 'yan Kwankwasiyya a ciki. Wataƙila mai gadi ɗan Kwankwasiyya ne, ko yaron gidan da yake dafa maka abinci ɗan Kwankwasiyya ne.
“Sai dai idan ya san kana da sha’awar tafiyar ne zai gaya maka, saboda ba ya son ya ɓata maka rai,”
In ji Kwankwaso
Samu sauyi a siyasar Najeriya
Kwankwaso ya ce yanzu bambancin fahimtar siyasa tsakanin tsofaffi da matasa a Najeriya ya zama abin da ba za a iya watsi da shi ba, yana mai cewa tsofaffin shugabannin ƙasar sun kasa fahimtar girman sauyin da ake samu.

Source: Facebook
Ya ce har yanzu wasu ’yan siyasa na mayar da hankali ne kan addini da ƙabila, abubuwan ba sa nuna yadda matasan Najeriya ke yanke shawarar zaɓe a yanzu.
“Mutanen da muke magana a kansu ma ba su fahimta. Wasu na magana kan addini, wasu na magana kan ƙabila. Amma matasa suna neman shugabanci nagari ga wannan ƙasa, kuma ina ganin suna da gaskiya ƙwarai,”
In ji shi.
Imran Muhammad ya wallafa bidiyon hirar Kwankwaso a X:
Kwankwaso ya goyi bayan Obi
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya amince da mika takarar jam'iyyar NDC zuwa Kudancin Najeriya a 2027.

Kara karanta wannan
NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya
Alamu sun nuna cewa hakan zai ba Peter Obi damar tsayawa takara a zaben 2027 kasancewar yana cikin manyan 'ya NDC da suka nuna sha'war hakan.
Kwankwaso da Obi sun shiga jam’iyyar NDC a hukumance ranar 3 ga Mayun 2026 bayan sun fice daga ADC sakamakon rikice-rikicen cikin gida.
Asali: Legit.ng
