'Kwankwasiyya Ce Ta Daga Abba': NDC na Shirin Fattakar Gwamnatin Kano a 2027

'Kwankwasiyya Ce Ta Daga Abba': NDC na Shirin Fattakar Gwamnatin Kano a 2027

  • Jam'iyyar adawa ata NDC ta ce ba ta da fargabar tunkarar babban zaɓen 2027 a Kano duk da APC ke mulki a sama da kasa
  • Mai magana da yawun NDC, Hon Yusuf Fasaha ya shaidawa Legit cewa Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓe ne saboda tasirin Kwankwasiyya
  • Ta bayyana dalilin da a ganinta zai sa NDC ta kwace mulki daga gwamnatin Abba duk da ya koma APC wacce ke mulkin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam'iyyar NDC a jihar Kano ta ce ba ta da wata fargaba game da babban zaɓen 2027, tana mai bayyana cewa ta shirya tsaf domin fafatawa da sauran jam'iyyu.

Mai magana da yawun jam'iyyar a Kano, Yusuf Fasaha, ya shaida wa Legit cewa tun da farko gwamnatin Kano ta samu nasarar lashe zaɓe ne sakamakon ƙarfin tafiyar Kwankwasiyya, ba wai saboda ɗan takararta kaɗai ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

NDC ta ce ba ta tsoron zaben 2027 a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusu tare, Kakakin NDC Yusuf Fasaha Hoto: Ibrahim Adam/Yusuf Fasaha
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da Daily Nigerian, Fasaha ya ce jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne babban ginshiƙin nasarorin da tafiyar ke samu a zaɓe.

NDC ta yi watsi da tasirin Abba

Hon Yusuf Fasaha ya kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba shi da wani tasiri da za a ce zai girgiza Kwankwasiyya da ita.

Ya ce:

"Ba ɗan takara ne yake kawo Kwankwasiyya ba. Wallahi Abba idan ka cire Kwankwasiyya ko Galadanci ba zai ci ba saboda ba shi da mu'amala."

Ya ƙara da cewa:

"Ba shi da wani tsari na siyasa ko na zaɓe."

NDC ba ta karya - Fasaha

Yusuf Fasaha ya ce tsarin siyasar NDC ya ginu ne kan faɗin gaskiya, yana mai cewa ko waɗanda suke adawa da su suna sanin cewa ba sa yin ƙage ko yaɗa ƙarya.

Fasaha ya ce alfarmar Kwankwaso ce ta ba Abba damar zama gwamna
Gwamnan Kano tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a baya Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewarsa, jam'iyyar na da ƙwarin gwiwar samun nasara a babban zaɓen 2027, saboda tana ganin ta tattara manyan jiga-jigan siyasa da za su ƙara mata ƙarfi, musamman a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Babban fasto ya fadi makomar Obi da Kwankwaso a zaben 2027

Ya bayyana cewa NDC ta yi imanin tana da duk abin da ake buƙata domin doke APC a zaɓe mai zuwa domin tana da magoya bayan da aka kwaso daga APC da kuma wanda Kwankwasiyya ke alfahari da su.

NDC ta gorantawa Hanga

A baya, kun samu labarin cewa jam'iyyar NDC a Kano ta fitar da sanarwa jim kadan bayan an fitar da sanarwar cewa Sanata Rufa'i Hanga ya fice daga cikinta da tsarin Kwankwasiyya.

Tun kafin a kawo wannan mataki, an ga yadda manyan APC suka rika zarya wurin Sanata Rufa'i Hanga domin a lallaba shi ya rabu da tsarin Kwankwasiyya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Mai magana da yawun jam'iyyar NDC, Yusuf Rabi'u Fasaha, ya ce wani lokaci rabuwa da ɗan siyasa na iya zama alheri idan aka gano illar da ke tattare da zamansa wanda zai iya cutar da siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng