Shettima da APC Sun Kawo Dalilan da za Su Sa a Goyi bayan Tinubu a 2027

Shettima da APC Sun Kawo Dalilan da za Su Sa a Goyi bayan Tinubu a 2027

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya mika fom din neman tsayawa takara da shugaba Bola Tinubu ya saya ga jam'iyyar APC
  • A wani taro da aka yi a Abuja, Shettima ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2027 domin a cewarsa ya kawo cigaba
  • Shugaba jam'iyyar APC na kasa ya halarci taron, inda ya bayyana cewa Bola Tinubu ya kawo cigaba sosai a shekara hudu da ya kusa cikawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya mayar da fom ɗin neman tsayawa takara na shugaban ƙasa a madadin Bola Tinubu.

Mayar da fom din ya shigar da shugaban ƙasa Bola Tinubu cikin tseren neman tikitin shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a hukumance.

Kara karanta wannan

Matasa sun yi cincirindo a gidan Jonathan kan zaben shekarar 2027, sun fadi bukatarsu

Nentawe Yilwatda da Kashim Shettima
Shugaban APC, Nentawe Yilwatda da Kashim Shettima a wajen taro a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wallafa a Facebook cewa an yi taron ne a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.

Maganar Shettima kan Tinubu

Da yake jawabi a wajen taron, Shettima ya ce mika fom sake tabbatar da amincewa ce ga shugaban ƙasa wanda ya ce ya nuna ƙwarewarsa a lokacin matsin lamba tare da fitar da Najeriya daga wani mawuyacin hali na tattalin arziƙi.

“Shugaban ƙasa ya cika alƙawarin samar da daidaito da farfaɗo da ƙasa. Kalubalen da suka faru a baya ba su raunana shi ba. Maimakon haka, sun mayar da shi gwarzon jam’iyya,”

In ji shi.

Yayin da ya ke nuna cewa Tinubu ya samu nasara, Shettima ya ce:

“Mun tsallaka tudun mun tsira. Mun fita daga duhu. Najeriya tana kan hanyar farfaɗowa da bunƙasa,”

A karshe Shettima ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da jam’iyya, addini ko yanki ba su mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai, an tayar da hargitsi a wurin taron jam'iyyar NDC a Enugu

Manyan APC a wajen taro a Abuja
Kashim Shettima, gwamnonin APC a wajen taro a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Bayanin shugaban APC na kasa

Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana taron a matsayin na ci gaba da jajircewa, bunƙasa abubuwan more rayuwa da sauye-sauyen tattalin arziƙi.

Ya kuma tunatar da ‘yan jam’iyyar cewa kwamitin zartarwa na ƙasa, NEC ya riga ya amince baki ɗaya da shugaba Tinubu domin wa’adi na biyu a taron da aka yi a bara.

“Dukkanmu da muke zaune a nan a matsayin mambobin NEC mun yanke shawara a bara cewa za mu goyi bayan Bola Tinubu,”

In ji Yilwatda.

Ya bayyana cewa cire buƙatar tantance shugaba Tinubu ne domin cika alkawarin wannan goyon bayan da aka nuna masa tun da farko.

Shettima ya yabawa Wadada

A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettim ya nuna goyon baya ga Ahmed Wadada a Nasarawa.

Yayin wani taron tattalin arziki a Nasarawa, Kashim Shettima ya bayyana cewa Sanata Wadada mutum ne da zai iya cirewa jihar kitse a wuta.

Sanata Wadada ne wanda gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya amince ya gaje shi a zaben 2027 duk da cewa wasu 'yan APC sun ce suna da ja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng