Tsohon Shugaban Kasa, Jonathan Ya Canza Jam'iyya don Ya Fito Takara a 2027? Gaskiya Ta Bayyana

Tsohon Shugaban Kasa, Jonathan Ya Canza Jam'iyya don Ya Fito Takara a 2027? Gaskiya Ta Bayyana

  • Jam'iyyar PDP tsagin Tanimu Turaki ta musanta fastocin Goodluck Jonathan da ake yadawa,da ke nuna ya koma wasu jam'iyyu daban-daban
  • PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar na nan a cikinta, kuma ya sabunta rijista a mazabarsa da ke jihar Bayelsa kwanan nan
  • Bangaren Turaki ya ce dole ne a yi wannan bayani saboda tanadin dokar zabe da ta haramta mutum ya yi rajista a jam’iyya fiye da daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsagin PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, cikakken mamba ne na jam’iyyar

Tsagin PDP ya tabbatar da cewa Jonathan ya halarci wurin aikin rajistar mambobi ta intanet da aka gudanar kwanan nan, kuma ya sabunta rijistarsa a hukumance.

Jonathan.
Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Twitter

Da gaske Jonathan ya sauya jam'iyya?

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Leadership ta ce PDP ta bayyana hakan ne yayin da ta karyata wasu fastocin yakin neman zabe da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadanda ke alakanta Jonathan da jam’iyyu daban-daban gabanin zaben 2027.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran bangaren, Ini Ememobong, ya fitar ranar Asabar, ya gargadi ’yan Najeriya da kada su danganta Jonathan da wata jam’iyya daban da PDP.

PDP ta ce fastocin bogi ne

Sanarwar mai taken “Ku yi hattara da fastocin yakin neman zaben GEJ na bogi” ta ce fastocin suna nuna hoton Jonathan shi kadai ko tare da wasu fitattun ’yan Najeriya a matsayin mataimakansa.

“An fara yada fastocin yakin neman zabe masu dauke da hoton tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ko shi kadai ko tare da wasu manyan mutane a matsayin abokan takara, a kafafen sada zumunta,” in ji sanarwar.

Bangaren PDP ya ce fastocin sun kuma nuna Jonathan a matsayin mamba na wasu jam’iyyun siyasa daban-daban, abin da ta ce ba gaskiya ba ne.

Jonathan ya yi rajista a PDP

Jam’iyyar ta jaddada cewa Jonathan har yanzu mamba ne na PDP karkashin shugabancin Turaki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Za a buga siyasa: Gwamnan Bauchi ya saye fom din neman takara a 2027

“Muna masu bayyana wa karara cewa Goodluck Ebele Jonathan cikakken mamba ne na PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, SAN,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa Jonathan da kansa ya yi rajista a mazabarsa yayin aikin rajistar mambobi ta zamani da aka kammala kwanan nan.

Shugaban PDP.
Shugaban tsagin jam'iyyar PDP, Kabiru Tanibu Turaki yana jawabi ga manema labarai a hedkwatar yan sandan Najeriya da ke Abuja Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP ta gargadi hukumar INEC

Bangaren Turaki ya ce dole ne a yi wannan bayani saboda tanadin dokar zabe da ta haramta mutum ya yi rajista a jam’iyya fiye da daya.

“Rajista a jam’iyya fiye da daya haramun ne kuma ana hukunta wanda aka kama da hakan,” in ji sanarwar.

PDP ta kuma yi zargin cewa wasu mutane na iya kokarin saka bayanan Jonathan da wasu fitattun ’yan siyasa cikin kundin rajistar wasu jam’iyyu ba tare da izininsu ba.

Jam’iyyar ta bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da jama’a su yi watsi da irin wadannan yunkuri, tana mai cewa duk wani mataki makamancin haka yaudara ce.

Jonathan ya yi magana kan takara

A baya, kun ji cewa tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi magana game da yiwuwar tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Wike vs Turaki: 'An ruguza yunkurin hana PDP tsaida dan takarar shugaban Kasa a zaben 2027'

Hakan na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da matasan Najeriya ke yi masa game da takarar shugaban kasa tun bayan barin mulki.

Jonathan ya ce ya fahimci bukatun da matasan suka gabatar masa, inda ya ce zai tuntubi mutane da dama tare da yin nazari sosai kafin daukar matakin da ya dace kan tsayawa takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262