Za a Buga Siyasa: Gwamnan Bauchi Ya Saye Fom din Neman Takara a 2027
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya saye fom din neman takara a zabe 2027 da ke tafe a Najeriya
- Bala Mohammed ya bayyana cewa siyasar Najeriya na cikin wani yanayi da ke hana mutane mutane masu nagarta neman shiga takara
- Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APM, inda ya sanar da cewa 'yan PDP za su shiga tafiyar a Bauchi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed ya saye fom ɗin neman tsayawa takarar Sanata a jam’iyyar APM kwanaki biyar bayan sauya sheka.
A ranar 2 ga Mayun 2026, Bala Mohammed ya shiga APM bayan ya fice daga PDP sakamakon shari’o’in kotu da rikicin cikin gida da suka addabi jam’iyyar.

Source: Facebook
Gwamna Bala Mohammed ya yi bayani game da taron da ya yi da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APM a wani sako da ya wallafa a Facebook.
Gwamnan Bauchi zai yi takara
Bala Mohammed ya ce APM ta nuna kanta a matsayin wata ingantacciyar jam’iyya da ba ta da matsalolin shari’a domin shi da magoya bayansa su ci gaba da yi wa al’umma hidima a cikinta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Bala Mohammed ya ce ya karɓi fom ɗin takarar Sanata ne yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa, NEC, na APM da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa.
“A yayin taron, na karɓi fom ɗina a hukumance domin tsayawa takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu ƙarƙashin inuwar APM a shirin zaɓe mai zuwa,”
In ji shi.
Bayani kan taron APM
Bala Mohammed ya ce taron NEC ɗin, wanda Yusuf Mamman Dantalle, shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya jagoranta, ya mayar da hankali ne kan muhimman batutuwan ƙasa da na jam’iyyar.
The Cable ta rahoto gwamnan Bauchi ya ƙara da cewa taron ya ba shi damar sanin tsarin shugabancin jam’iyyar a hukumance.
Ya ce yanayin siyasar Najeriya ya ƙara fuskantar ƙalubale sakamakon halayen rashin kishin dimokuraɗiyya da barazanar siyasa, waɗanda a cewarsa suka sa hana jama'a masu nagarta su shiga a dama da su.
Bala Mohammed ya ce bayan tattaunawa mai faɗi da abokan siyasa, masu ruwa da tsaki da magoya baya a faɗin ƙasa, APM ce ta fito a matsayin jam’iyyar da ta fi dacewa da hangen nesansu da burinsu na bai ɗaya.

Source: Facebook
Gwamnan ya ce jam’iyyar tana da dabi’u iri ɗaya da mahangar siyasarsa, musamman a fannoni kamar shugabanci nagari, girmama dimokuraɗiyya, adalci, haɗin kai da mutunta doka.
Korafin gwamnan Bauchi ga INEC
A wani labarin, kun ji cewa gwamna Bala Mohammed ya yi korafi game da yadda jadawalin zaben 2027 zai gudana a lokacin aikin Hajji.
Bala Mohammed ya bayyana cewa bai kamata a sanya jadawalin zaben 2027 a lokacin Hajji ba, inda yace lokacin zai yi karo da ranar Arafa.
A kan haka ya yi kira ga shugaban hukumar zabe ta kasa da shugaban kasa Bola Tinubu da su yi magana a daga lokacin zabe fitar da gwani a Najeriya.
Asali: Legit.ng

