Yadda Za Ku Duba Sunayen Waɗanda Hukumar Kwastam Ta ɗauka Aiki a 2026

Yadda Za Ku Duba Sunayen Waɗanda Hukumar Kwastam Ta ɗauka Aiki a 2026

Abuja - Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a aikin ɗaukar ma'aikata na shekarar 2024/2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

Hukumar Kwastam ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasarar samun aiki a 2026
Shugaban Kwastam yana zagayen sashen rundunar na Apapa da ke Legas. Hoto: Nigeria Customs Service
Source: Twitter

Yadda za ku duba sunaye da mataki na gaba

Adewale Adeniyi ya bayyana cewa mutum 3,852 ne suka samu nasara daga cikin mutum 573,680 da suka nemi aikin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kwanturolan hukumar ya kuma bayyana cewa wannan na daga cikin mafi tsananin gasar daukar aiki da aka taɓa yi a tarihin hukumar.

Hukumar ta bukaci duk wanda sunansa ya fito cikin jerin sunayen da aka fitar da ya bi waɗannan matakai:

1. Duba sunanka a shafin NCS

Kara karanta wannan

Kwastam ta faɗi lokacin da za ta dauki ma'aikata a 2026, ta sauya tsarinta

Masu neman aikin su shiga shafin yanar gizon Hukumar Kwastam domin duba ko sunayensu suna cikin jerin waɗanda suka yi nasara.

Haka kuma, su riƙa duba adireshin imel da lambar wayar da suka yi amfani da su wajen yin rajista domin samun ƙarin umarni daga hukumar.

2. Shiga shafin sabunta bayanai

Bayan tabbatar da cewa sunanka ya fito, sai ka shiga shafin sabunta bayanan Hukumar Kwastam ta amfani da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) ko adireshin imel da ka yi rajista da shi.

3. Dora takardar shaidar lafiyarka

Hukumar ta umarci duk wanda ya samu nasara da ya loda ingantacciyar takardar shaidar lafiyar jiki daga asibitin gwamnati ko wanda gwamnati ta amince da shi.

An bukaci a kammala wannan kafin ranar 5 ga Agusta, 2026.

4. Sabunta jihar da kake zaune

Masu nasara za su sabunta bayanin jihar da suke zaune a halin yanzu cikin tsarin da hukumar ta tanada.

5. Amince da tayin aikin

Bayan kammala dukkan matakan da aka bukata, sai a danna maɓallin "Accept Offer" domin amincewa da tayin aikin.

Kara karanta wannan

An kashe dan siyasa da 'yan bindiga suka kai kazamin hari Filato da dare

6. Jira lambar TIN

Hukumar ta ce bayan kammala waɗannan matakai, za a tura wa masu nasara lambar Trainee Identification Number (TIN).

Ta ƙara da cewa za ta sanar da masu nasara cikakken bayani kan tantancewa, wuraren da za a gudanar da ita da sauran buƙatun da suka rage ta hanyoyin sadarwar ta na hukuma.

An bukaci wadanda suka samu aikin su jira a tura masu lambar TIN
Hukumar Kwastam ta gudanar da bita ga ma'aikatanta. Hoto: Nigeria Customs Service
Source: Facebook

Mutum 3,852 ne suka samu nasara

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa hukumar Kwastam ta bayyana cewa mutum 3,852 ne suka samu nasara a rukunonin ɗaukar ma'aikata uku.

Daga cikin su, mutum 1,275 sun shiga rukunin Superintendent Cadre, mutum 367 sun shiga Inspectorate Cadre, yayin da mutum 2,210 suka samu gurbi a Customs Assistant Cadre.

Hukumar ta ce adadin ya nuna cewa kashi 0.67 cikin 100 kacal ne suka samu nasara daga cikin dukkan mutum 573,680 da suka nemi aikin.

Kwastam ta saki sunaye

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar Kwastam ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara a daukar ma'aikatan ASC II na shekarar 2024/2025.

Kara karanta wannan

Siyasa ta fara zafi, gwamna ya yi tsaurin ido ya gargadi Tinubu kan zabe

An umurci wadanda suka yi nasara su loda takardar shaidar lafiyarsu daga ranar 29 ga Yuli, 2026 cikin mako guda.

Hukumar ta gargadi masu nasara cewa rashin bin umarnin da aka gindaya na iya jawo soke tayin aikin da aka ba su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com