Kotu Ta Hana Tsohon Gwamna Shiga Zaben 2027 da Za a Yi Gaba Ɗaya

Kotu Ta Hana Tsohon Gwamna Shiga Zaben 2027 da Za a Yi Gaba Ɗaya

  • Kotun Tarayya da ke Jalingo a jihar Taraba ta yi hukunci kan karar da aka shigar da tsohon gwamnan jihar Rabaran Jolly Nyame
  • Wata kungiya ta shigar da Nyame kara ne kan takarar zaben 2027 saboda hukuncin da aka taba yanke masa kan rashawa
  • Mai shari’a Mashkur Salisu ya bayyana cewa afuwar shugaban kasa da aka bai wa Nyame a 2022 ba ta dawo masa da damar shiga zabe nan take ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Kotun Tarayya da ke Jalingo ta yanke hukunci kan shari'ar da ake yi da cewa tsohon gwamnan Taraba, Rabaran Jolly Nyame.

Kotun ta yanke hukunci cewa Nyame ba zai iya shiga zaben shekarar 2027 ba saboda hukuncin cin hanci da rashawa.

Nyame ya samu matsala kan siyasarsa a zaɓen 2027
Tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame yayin da yake gidan yari. Hoto: Rev. Jolly Nyame.
Source: Getty Images

Mai shari’a Mashkur Salisu ya bayyana hakan ne a karar da kungiyar Taraba Progress Front ta shigar, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Kotu ta shirya yanke hukunci kan hallacin shiga takarar Jonathan a 2027

Ƙungiya ta maka Nyame a kotu kan takara

Kungiyar tana neman karin haske kan matsayin Nyame bayan afuwar shugaban kasa kan tuhumar cin hanci da rashawa.

Kotun ta ce afuwar shugaban kasa da aka bai wa Nyame a shekarar 2022 saboda matsalar lafiya ba cikakkiyar afuwa ba ce kamar yadda doka ta tanada.

Lauyan Abuja, Barrister Badmus, ne ya nemi kotun ta fayyace tasirin hukuncin da aka taba yankewa Nyame da kuma afuwar shugaban kasa da aka ba shi.

Kotun ta yi nuni da sashe na 182(1)(e) na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma sashe na 85 na dokar zabe ta 2022 wajen yanke hukuncin.

Mai shari’ar ya kuma yi dogaro da hukuncin babbar kotun Abuja na shekarar 2018 wanda ya samu Nyame da laifin rashawa da karkatar da kudaden gwamnati.

Kotun ta bayyana cewa duk da afuwar shugaban kasa, har yanzu akwai sharuddan kundin tsarin mulki da suke hana Nyame shiga zabe kafin wa’adin shekaru goma.

Kara karanta wannan

Nasir El Rufai ya sake cin karo da matsala, ICPC ta yi fatali da bukatarsa

Kotu ta kawo hujjojin hana Nyame takara a 2027
Tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame a Jalingo. Hoto: Rev. Jolly Nyame.
Source: Facebook

Wace shekara Nyame zai iya sake takara?

A cewar kotun, Nyame ba zai samu damar sake tsayawa takara ba sai bayan shekarar 2028 saboda wa’adin da doka ta shimfida kan irin wannan hukunci.

A gefe guda, jam’iyyar APC a Taraba ta musanta rade-radin cewa akwai sabani tsakanin Gwamna Agbu Kefas da tsohon gwamna Jolly Nyame kan siyasar 2027.

Sakataren yada labaran APC a Taraba, Aaron Aritmas, ya ce babu wata alama da ke nuna cewa an hana Nyame neman kowace kujera ta siyasa.

Aritmas ya ce Gwamna Kefas na ci gaba da mutunta Nyame a matsayin daya daga cikin wadanda suka kafa tubalin siyasar Taraba tun farko.

A cewarsa, idan Nyame yana son tsayawa takara, wannan hakkinsa ne na kundin tsarin mulki, kuma babu wanda ya fito karara ya hana shi yin hakan.

Yayan tsohon gwamnan Bayelsa ya mutu

An ji cewa yayan tsohon gwamnan Bayelsa kuma tsohon karamin ministan man fetur, a Gwamnatin tarayya Timipre Sylva, ya rasu.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Hadimin Timipre Sylva mai suna Julius Bokoru ya sanar da rasuwar marigayin tare da bayyana shirye-shiryen gudanar da zaman makoki.

Rahotanni sun nuna cewa za a fara gudanar da taron Duwei Wari domin karrama marigayin daga ranar Laraba a jihar Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.