Yaki na Shirin Dawowa: An Zargi Iran Ta Harba Makamai Masu Linzami UAE

Yaki na Shirin Dawowa: An Zargi Iran Ta Harba Makamai Masu Linzami UAE

  • Rikici na kara zafafa a Gabas ta Tsakiya tun bayan da shugaban Amurka ya yi barazanar cewa zai tanadi sojoji su rika raka jiragen ruwa a Hormuz
  • An samu rahotannin harba makamai masu linzami a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda gwamnatin kasar ta zargi Iran da kai mata harin
  • Yayin da ake cigaba da tantance barnar da harin ya yi, gwamnatin Iran ta nesanta kanta da shi, inda ta ce Amurka ce za ta iya kai harin ba ita ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta zargi Iran da kai mata hare-hare da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka.

Lamarin da ya haddasa gobara a wata matatar mai a masarautar Fujairah da ke gabashin kasar, tare da jikkata ‘yan kasar Indiya uku.

Kara karanta wannan

Iran ta kai farmaki kan jirgin ruwan Amurka a kusa da mashigar Hormuz

Wani hari da aka kai kasar UAE
Hayaki na tashi a wani waje da aka kai hari a UAE. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An fara kai hari bayan sulhu

Tashar DW ta wallafa cewa hare-haren da aka kai a ranar Litinin su ne na farko a UAE tun bayan da Iran da Amurka suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilu, 2026.

Sun zo ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da wani sabon yunkuri na rakiyar tankokin mai da suka makale domin su fita daga mashigar Hormuz.

Rundunar hadin gwiwar sojojin Iran ta gargadi jiragen kasuwanci da su guji amincewa da tayin Amurka, tana mai cewa dakarun Amurka za su kai su su baro su.

An kai hare-hare kasar UAE

Ma’aikatar tsaron UAE ta ce tsarin kariyar sararin samanta ya “tarwatsa” makamai masu linzami 16 da kuma jiragen yaki marasa matuka hudu da aka harba daga Iran a ranar.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da ta kira:

“Mummunan hari na ta’addanci ba tare da wani dalili ba da Iran ta sake kai wa, wanda ya nufi wuraren fararen hula da kayayyakin more rayuwa a kasar.”

Kara karanta wannan

Lamari zai dagule: Iran ta ja kunnen Trump game da tura sojoji Hormuz

Ta ce ba za ta lamunci duk wata barazana ga tsaro da ikon kasarta ba, tare da gargadin cewa tana da cikakken hakki na halal na mayar da martani kan hare-haren.

Ga bidyon harin da Al Jazeera ta wallafa a X:

Iran ta musanta kai hari UAE

Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya ambato wani jami’in soja da bai bayyana sunansa ba yana cewa Iran bata kai hari wata kasa ba.

Ya ce

“Iran ba ta da wani shiri na kai hari kan wadannan wuraren mai da aka ambata.”

Ya danganta lamarin da:

“Tsoma bakin Amurka domin kirkirar hanya ga zirga-zirgar jiragen ruwa ba bisa ka’ida ba ta cikin mashigar Hormuz.”
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian
Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran na magana a taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Majiyar ta kara da cewa :

“Ya kamata a daura alhakin wannan kan sojojin Amurka.”

An yi harbi a fadar Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa jami'an leken asirin Amurka sun tabbatar da cewa an yi harbe-harbe a kusa da fadar shugaba Donald Trump.

Wan jami'in leken asiri ya yi karin bayani da cewa an hango wani mutumi da bindiga kuma da aka nemi tsayar da shi ya fara harbi.

Sai dai ya kara da cewa jami'an Amurka sun mayar da martani da bude masa wuta, inda suka harbe shi kuma yana asibiti yana karbat magani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng