Duniya Labari: Yayan Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Duniya Labari: Yayan Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon gwamnan Bayelsa kuma tsohon karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya rasa babban yayansa
  • Wani hadimin Timipre Sylva mai suna Julius Bokoru ya sanar da rasuwar marigayin tare da bayyana shirye-shiryen gudanar da zaman makoki
  • Rahotanni sun nuna cewa za a fara gudanar da taron Duwei Wari domin karrama marigayin daga ranar Laraba a jihar Bayelsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yenagoa, Bayelsa - An shiga jimami bayan rasuwar Cif Johnbull Anagha Sylva, babban yayan tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva.

Timipre Sylva ya taba rike mukamin gwamnan Bayelsa sannan kuma ya yi aiki a matsayin karamin ministan man fetur a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

Tsohon gwamna ya yi babban rashi a rayuwarsa
Tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva. Hoto: Timipre Marlin Sylva.
Source: Facebook

Julius Bokoru, daya daga cikin hadiman tsohon ministan, ne ya sanar da rasuwar marigayin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba 6 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

A karon farko, Ganduje ya amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

Zargin da ake yi wa Timipre Sylva

Wannan abin bakin ciki na zuwa ne yayin da ake tuhumar kanin marigayin kuma tsohon minista a Najeriya da hannu a yunkurin juyin mulki a kasar.

Sylva na daga cikin wadanda aka shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja wanda ya ba mutane da dama mamaki.

Binciken da jami'an tsaron Najeriya ke ci gaba da yi ya gano Sylva da zargin ɗaukar nauyin shirin juyin mulki inda aka gano ya bayar da N785m daga cikin kudin da aka fitar.

Ana zargin Sylva da hannu a yunkurin juyin mulki
Wasu mutanen da ake zargi a yunkurin kifar da Bola Tinubu. Hoto: Zawiyar Sheikh Sani Khalifa Zaria, Timipre Sylva, Zagazola Makama.
Source: Facebook

Yayan tsohon gwamna ya mutu a Najeriya

A cewar Bokoru, marigayin ya rasu ne ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026, abin da ya jefa iyalai da makusanta cikin alhini.

Sanarwar ta bayyana cewa za a fara gudanar da zaman makoki na kwanaki uku wanda aka fi sani da Duwei Wari domin girmama marigayin.

Yadda aka tsara zaman makoki a Bayelsa

An bayyana cewa za a fara taron tun daga karfe uku na yammacin ranar Laraba 6 ga watan Mayun 2026 domin bai wa jama’a damar yi wa iyalan ta’aziyya.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawakin gargajiya a Arewa, Mai Asharalle ya yi bankwana da duniya

Bokoru ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga iyalan Sylva da kuma al’ummar da suka san marigayin a rayuwarsa.

Ya ce:

“Cikin bakin ciki muke sanar da rasuwar Cif Johnbull Anagha Sylva, babban yayan mai girma Timipre Marlin Sylva.”

Rahoton ya nuna cewa mutane da dama sun fara mika sakonnin ta’aziyya ga tsohon gwamnan Bayelsa da sauran iyalansa bayan samun labarin rasuwar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin rasuwar marigayin ba daga bangaren iyalansa ko makusantansa.

Juyin mulki: An gurfanar da Sylva a gaban kotu

A baya, an ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu mutane da ake zargi suna da hannu a yunkurin juyin mulki a shekarar 2025.

Cikin wadanda aka gurfanar akwai tsohon ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva da malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa daga Zaria a jihar Kaduna.

Gwamnatin tarayya ta zargi wasu daga cikinsu da rashin sanar da hukumomi shirye-shiryen juyin mulki da kuma karbar kudi ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.