Ina bukatar jike-jiken gargajiya - Nyame ya roki kotu daga gidan yari

Ina bukatar jike-jiken gargajiya - Nyame ya roki kotu daga gidan yari

Tsohon gwamnan jihar Taraba da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 14, Jolly Nyame ya garzaya babban kotun tarayya da ke Gudu, Abuja inda ya nemi a bayar da belinsa duk da an zartar masa da hukunci.

Ya ce yana bukatar belin ne saboda ya samu ya karbo magunguna gargajiyarsa da ya ke amfani dashi wajen maganin cutar suga da hawan jini tun kafin a yanke masa hukuncin a ranar 30 ga watan Mayun 2018.

Lauyan Nyame, Mr. Olalekan Ojo ya shaidawa alkalin kotun Justice Adebukola Banjoko wadda ta yanke wa tsohon gwamnan hukunci cewa Nyame ya kwashe shekaru 10 yana fama da cututukan suga da hawan jinin.

Ina bukatar jike-jiken gargajiya - Nyame ya roki kotu daga gidan yari

Ina bukatar jike-jiken gargajiya - Nyame ya roki kotu daga gidan yari

Ojo ya ce tunatar da kotun game da rahoton rashin lafiya da asibitin Jalingo na jihar Taraba ta bayar a ranar 19 ga watan Yuni game da tsohon gwamnan inda ya ce gwamnan na iya rasa ransa idan ba'a bashi dama ya tafi neman maganin ba.

KU KARANTA: Kiristoci sunyi zanga-zanga a Jos, kalli hotuna

Ya kuma ce Nyame ya bukaci masu tsaron kurkukun kuje da ke Abuja su bashi daman ya sha maganin gargajiyar sai dai basu amince masa ba.

Ojo ya fadawa kotu cewa rashin lafiyar da neman maganin gargajiya karfafan dalilai ne da ya dace a bawa mutum beli don ya ceto lafiyarsa.

Lauyan EFCC, Mr. Rotimi Jacobs (SAN) ya roki kotu tayi watsi da bukatar na tsohon gwamnan.

Ya ce Nyame a matsayinsa na wanda aka yanke wa hukunci ya rasa damarsa ne fita waje neman magani illa magungunan da gidan fursunan ta samar.

Ya kara da cewa ana iya bashi damar ya fita waje neman magani ne kawai idan hukumar gidan yarin ta ce ba ta da magungunan kula da irin rashin lafiyar da wanda aka yanke wa hukunci ke fama da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel