Nasir El Rufai Ya Sake Cin Karo da Matsala, ICPC Ta Yi Fatali da Bukatarsa

Nasir El Rufai Ya Sake Cin Karo da Matsala, ICPC Ta Yi Fatali da Bukatarsa

  • Hukumar ICPC ta shigar da takardar martani a gaban kotu tana adawa da sabon bukatar beli da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gabatar
  • Babbar Kotun Kaduna ta dage sauraron karar neman belin El-Rufai zuwa ranar 13 ga Mayu bayan ICPC ta nemi karin lokaci domin nazarin sabbin takardu
  • Kotu ta taba kin bayar da beli ga El-Rufai bisa zargin yiwuwar tserewa, hana bincike gudana da kuma yiwuwar yin tasiri kan shaidu da hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Hukumar ICPC ta bayyana adawarta ga sabon bukatar beli da tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya sake gabatarwa a gaban Babbar Kotun Kaduna.

A zaman sauraron karar ranar Talata, lauyan Nasir El-Rufai, Ubong Akpang, ya shaida wa kotu cewa sun shigar da sabon bukatar beli saboda batun ‘yancin wanda ake kara.

Kara karanta wannan

Pantami zai yi yaki da zalunci wajen fitar da dan takarar gwamnan APC a Gombe

ICPC ta yi fatali da bukatar Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Lauyan ya bayyana cewa sun kammala gabatar da dukkan takardun da ake bukata tare da mika su ga bangaren masu kara domin a ci gaba da sauraron karar, cewar Tribune.

El-Rufai: Abin da lauyan ICPC ya ce

Sai dai lauyan ICPC, Ibrahim Mukhtar, ya bayyana wa kotu cewa yanzu aka mika masa karin takardar bayanin goyon bayan bukatar belin.

Mukhtar ya bukaci kotu ta ba shi lokaci domin yin nazari a kan sabbin takardun kafin a ci gaba da sauraron karar.

Bayan sauraron bangarorin biyu, kotun ta dage karar zuwa ranar 13 ga watan Mayun 2026 domin sauraron sabon bukatar beli.

Tun da farko, kotun ta ki bayar da beli ga El-Rufai a wata bukata da ya gabatar saboda wasu sabbin bayanai da ICPC ta gabatar.

Mai shari’a D.H. Khobo ya ce El-Rufai bai gabatar da wata takardar da za ta kalubalanci zarge-zargen da ICPC ta yi a gabansa ba.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Hukumar ICPC ta zargi tsohon gwamnan da yiwuwar tserewa saboda tasirinsa da karfinsa, tare da zargin hana jami’ai kama shi a filin jirgin Abuja.

El-Rufai ya rasa damar ba da belina a shari'ar da ake yi
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai yayin ganawa da manema labarai a Kaduna. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Abin da ICPC ke zargin El-Rufai da aikatawa

Hukumar ta kuma ce El-Rufai ya ki mika takardun tafiyarsa da wasu na’urori da ake bukata domin gudanar da bincike, kamar yadda Punch ta ce.

Kotun ta bayyana cewa bayar da beli yana karkashin ikon kotu ne, kuma dole a tabbatar da cewa hakan zai amfani shari’a.

Mai shari’a Khobo ya ce matsayin El-Rufai a siyasa na iya sa ya yi tasiri kan bincike musamman ganin wasu da ake zargi har yanzu suna waje.

Kotun ta kuma yi watsi da zargin rashin lafiya da aka gabatar domin neman beli saboda babu isassun hujjojin da suka tabbatar da hakan.

Saboda haka, kotun ta umurci a ci gaba da tsare El-Rufai a hannun ICPC har zuwa lokacin da za a fara shari’ar cikin gaggawa.

Duk da wannan hukunci, bangaren lauyoyin El-Rufai ya sake shigar da sabon bukatar beli domin kotu ta sake nazarin lamarin.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Kotun Koli ta dage shari'ar rikicin sarautar Kano zuwa bayan zaben 2027

Ana shirya wa Malam El-Rufai makarkashiya

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya nuna damuwa kan sabon shirin da ya yi zargin ana kullawa a kansa.

El-Rufai ya nuna cewa ana yin wata kulla-kulla domin ganin an ci gaba da tsare shi a hannun hukumomi.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa ana kokarin alakanta da wasu laifuffuka domin ganin ya gaza samun beli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.