Dalilin da Yasa ba Zamu Saki Nyame da Dariye ba Duk da Anyi Musu Rangwame, Hukumar Gidajen Gyaran Hali

Dalilin da Yasa ba Zamu Saki Nyame da Dariye ba Duk da Anyi Musu Rangwame, Hukumar Gidajen Gyaran Hali

  • Bayan watanni biyu da fadar shugaban kasa tayi wa masu laifi 159 da ke tsare a gidan gyaran hali rangwame, duk da tsohon gwamnan Fulatu da tsohon gwamnan Taraba, har yanzu ana cigaba da tsaresu
  • Bayan an yi wa masu laifin rangwame, an gano yadda har yanzu ake cigaba da tsaresu a gidan gyaran halin, wanda hakan ya fusata wasu daga cikin'yan uwan tsohon gwamnan Fulatu tare da yin Allah wadai da halin da gwamanatin tarayya ta nuna kan lamarin
  • Sai dai, yayin da aka tuntubi kakakin hukumar gidajen gyaran halin, Abubakar Umar, cewa ya yi a yanzu ba za su iya sakin biyun ba sai sun samu takarda daga ma'aikatar shari'a tare da bada umarnin yin hakan

Har yanzu ba a sake su ba, bayan watanni biyu da yi wa masu laifi 159 rangwame, duk da tsohon gwamnan jihar Filatu, Sanata Joshua Dariye da tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame.

Kara karanta wannan

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

Majalisar tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar 14 ga watan Afirilu ta amince da yi wa masu laifin rangwame, wanda hakan ya jawo cece-kuce.

Joshua Dariye da Jolly Nyame
Dalilin da Yasa ba Zamu Saki Nyame da Dariye ba Duk da Anyi Musu Rangwame, Hukumar Gidajen Gyaran Hali. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Nyame na zaune a gidan gyaran hali bayan yanke masa hukuncin shekaru 12 bisa yin sama da fadi da N1.64 biliyan yayin milkinsa a matsayin gwamnan jihar Taraba, yayin da aka yankewa Dariye hukuncin shekaru 10 a gidan gyaran hali bisa kama shi da laifin almundahanar N1.126 biliyan.

Yayin bayyana dalilin yin rangwamen, babban hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya ce, zai zamo rashin tunani a ce an ki yi wa biyun rangwame duba da yadda suke fama da cutukan da barazana ne ga rayukansu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, binciken da Punch ta yi ranar Juma'a ya tabbatar da yadda ake cigaba da tsare biyun da sauran da gwamnatin tarayya tayi wa rangwame.

Kara karanta wannan

Borno: 'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Farmaki Sansanin Sojoji, Sun Yi Awon Gaba da Makamai

Sai dai, bayan an tuntubi kakakin hukumar gidan gyaran halin Najeriya, Abubakar Umar, bisa dalilin da yasa ake cigaba da tsare tsoffin gwamnonin biyu, ya bayyana yadda NCS bata da alhakin jinkirin.

Kamar yadda ya bayyana, hukumar gidan gyaran halin ba za ta iya sakin biyun ba har sai ma'aikatar shari'a ta rubuto musu takarda tare da nuna bukatar hakan.

A cewar Umar, "Dalilin da yasa ba a sake su ba saboda har yanzu muna jiran umarni daga ma'aikatar shari'a. Da zarar mun samu wannan, za mu yi hanzarin sakinsu. Shugaban kasa ne ya musu rangwame, babu shakka, amma dole a samu takarda da za ta goyi bayan sakinsu. Ba za a iya sakinsu daga sanar da hakan kawai ba."

Iya kokarin da aka yi don samun martanin ma'aikatar ta hannun hadimin ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Umar Gwandu, bai yi tasiri ba. Bai amsa kiraye-kirayen da aka yi masa ta waya ba kuma bai turo da amsar sakon da aka tura masa kan batun ba.

Kara karanta wannan

Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu

Sai dai kuma, karamar hukumar Bokko a jihar Fulatu ta bayyana tsananin rashin jinbdadinsu bisa kin sakin Dariye da cibiyar gyaran halin tayi.

Wasu 'yan uwan Dariye, wadanda suka rike kujerar gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007 'yan asalin yankin Mushere na karamar hukumar Bokkos sun yi Allah wadai da yadda gwamanatin tarayya ta nuna game da lamarin, inda suka siffanta cigaba da tsaresa a matsayin abun da bai dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel