Bayan Shan Suka, Gwamna Abba Ya Kare Matakin ba 'Yan APC Sama da Filaye 1500

Bayan Shan Suka, Gwamna Abba Ya Kare Matakin ba 'Yan APC Sama da Filaye 1500

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce rabon filaye na da nufin rage ƙarancin gidaje da samar da arziki ga iyalai
  • Abba Kabir Yusuf ya ce shirin zai bai wa matasa, mata da masu rauni damar gina kyakkyawar makoma
  • Wasu mazauna Kano sun soki rabon filaye da kuɗi ga shugabannin Ƙungiyar Yan’akwati na jam'iyyar APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan rabon filayen da gwamnatinsa ta yi.

Gwamna Abba ya ce rabon filayen ga jama'a da gwamnatinsa ke yi na da nufin rage ƙarancin gidaje, samar da arziki ga iyalai da kuma kafa tubali mai ƙarfi domin kyakkyawar makoma.

Gwamna Abba ya kare matakin raba filaye
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar, wadda jaridar The Punch ta samu a ranar Lahadi, 2 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Malami ya bankado 'sirrin' Tinubu game da neman cin zabe ta kowace hanya

A baya-bayan nan, Gwamna Abba ya raba filaye 1,540 tare da Naira miliyan 100 ga shugabannin Ƙungiyar Magoya Bayan Jam'iyyar APC ta rumfunan zaɓe, wadda aka fi sani da Yan’akwati.

Matakin ya jawo suka daga wasu mazauna jihar Kano, inda suka bayyana shi a matsayin cin hanci gabanin babban zaɓen 2027.

An raba takardun mallakar filaye

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana manufar shirin ne yayin rabon takardun mallakar filaye ga manyan mataimaka na musamman, manyan masu ba da rahoto na musamman, mataimaka na musamman, masu ba da rahoto na musamman da mataimaka na kai.

An gudanar da rabon ne ƙarƙashin kulawar Ma'aikatar Filaye da Tsara Birane, a zauren Coronation da ke Fadar Gwamnatin Jihar Kano ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026.

Sakataren gwamnatin jihar, Umar Ibrahim, ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron.

Sanarwar ta ruwaito gwamnan yana cewa:

“Samun filin gini a wani yanki da gwamnati ta tsara ba ƙaramin abu ba ne."

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda aka kama mutum 2 da zargin cefanar da filayen gwamnatin Kano

“Wannan shiri ba wai kawai na rabon filaye ba ne. Yana da nufin rage ƙarancin gidaje, ƙarfafa al'umma ta hanyar mallakar kadarori, samar da arziki ga iyalai da kuma bai wa matasa, mata da masu rauni tubali mai ƙarfi da za su gina kyakkyawar makoma a kai.”

Gwamnati ta cika alkawari

Gwamna Abba ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta yi imanin cewa ba a auna shugabanci da alkawuran da ake yi kawai ba, sai dai da yadda ake cika su.

Ya ce gwamnatin ta cika alkawarin da ta ɗauka ga waɗanda suka amfana da shirin.

Gwamnan ya yaba wa waɗanda suka samu filayen saboda goyon bayan da suka bai wa gwamnatinsa tun lokacin yaƙin neman zaɓe har zuwa yanzu.

Ya kuma roƙe su da su ɗauki kansu a matsayin jakadun gwamnatinsa, ta hanyar ci gaba da wayar da kan jama'a kan shirye-shirye da ayyukan da gwamnatin jihar ke gudanarwa.

Gwamna Abba ya raba filaye a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

An kwatanta rabon filaye

A nasa jawabin, kwamishinan filaye da tsara birane, Alhaji Abduljabar Umar, ya ce adadin filayen da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta raba ya zarce waɗanda gwamnatocin tsofaffin gwamnonin Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje, suka raba.

Ya shawarci waɗanda suka amfana da shirin da kada su sayar da filayen, sai dai su riƙe su domin amfanin gaba.

Kara karanta wannan

Badakalar PFIPC: 'Yan sanda sun kasa kawo Adeniyi gaban Majalisa, an ji dalili

Gwamnatin Abba ta bayar da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta miƙa tallafi ga iyalan marigayi Sufeto Sani Haladu, ɗan sanda da ya rasu yana bakin aiki a ranar 27 ga Maris, 2026.

Tallafin gwamnatin ya ƙunshi gudummawar kuɗi har N1m da kuma kayan abinci da suka haɗa da buhunan shinkafa biyar, buhunan taliya shida, buhunan makaroni shida da kuma jarkoki biyu na man girki mai ɗaukar lita 25 kowanne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng