Labaran tattalin arzikin Najeriya
Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da yin watsi da manoma, yayin da cinikayyar noma ta koma gibin N56.13bn daga rarar N740.27bn cikin shekara guda.
Abuja da jihohi 11 sun tashi da sama da Naira tiriliyan 4 daga rabon FAAC a bara. Sauran jihohi masu arzikin mai sun samu akalla nunkin N279bn da aka ba Kano.
Bankin Duniya ya ƙara hasashen ci gaban tattalin arzikin Najeriya zuwa kashi 4.3 a 2026, amma ya yi gargadin tasirin kashe kuɗin gwamnati gabanin zaɓen 2027.
Gwamnatin jihar Kwara za ta sayi hannun jarin matatar Dangote ga mata malamai, tare da bai wa fitattun masu yi wa ilimi hidima kyaututtukan N120m.
A jawabin Shugaba Bola Tinubu na Ranar Samun 'Yancin Kai, ya tabbatar wa 'Yan Najeriya cewa shekaru uku na gwagwarmayar sauye-sauyen tattalin arziki sun kawo nasara.
Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta kai matakin sauyi, bayan tattalin arziki ya ƙaru, hauhawar farashi da satar mai suka ragu sosai domin inganta kasa.
Bola Tinubu ya ce rage tsadar rayuwa shi ne babban fifikon gwamnatinsa, yana mai bayyana matakan rage kuɗin abinci, sufuri domin saukaka wa yan kasa.
Mazauna Osogbo a Osun sun kwashe kayan abinci daga rumbun wani shirin sayar da abinci mai rahusa bayan masu gudanar da shi sun ɓace da kuɗin jama’a.
Aliko Dangote ya bayyana dalilin da ya sa jikansa na farko baya son shiga kamfanin yanzu, yana son samun ƙwarewar aiki da harkokin kuɗi kafin komawa kamfanin.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari