Gwamna Sule Ya Fadi Dalilin Nuna Magajinsa da Ya Rikita APC a Siyasar Nasarawa

Gwamna Sule Ya Fadi Dalilin Nuna Magajinsa da Ya Rikita APC a Siyasar Nasarawa

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana dalilin zaban Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin magajinsa
  • Abdullahi Sule ya ce ya yi hakan ne bayan tuntuba mai zurfi, yana mai cewa burinsa shi ne samun ɗan takarar da zai fi sauƙin cin zaɓe
  • Ya jaddada cewa tsarin rabon mulki ya shafi yankuna, inda ya bayyana shekarun da yankin Keffi da Lafia suka shafe a kan mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sake yin magana bayan nuna wanda ya ke son ya gaje shi.

Gwamna Sule ya fito ya bayyana dalilin da ya sa ya ke son Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya kasance magajinsa a Nasarawa.

Gwamna Sule ya magantu kan nuna magajinsa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yayin taro a Lafia. Hoto: Gov. Abdullahi A Sule Mandate.
Source: Facebook

Gwamna Sule ya magantu kan magajinsa a Nasarawa

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Peter Obi ya bayyana dalilin ganawa da Jonathan

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin Gov. Abdullahi Sule Mandate ya wallafa a Facebook wanda ya yadu a kafofin sadarawa.

Gwamna ya ce ya duba cancantar wanda ya zaba ne domin samun saukin cin zabe ba tare da wata matsala ba.

Ya ce:

"Lokacin da na ke tuntuba, na je na nemo wadanda idan muka ba su wannan mulki za su iya rikewa, a zuciya na ce ina son yin adalci.
"Yankin Keffi sun yi shekaru takwas, Lafia sun yi 12 sai mu kuma za mu yi shekaru 8, idan ina son adalci sai in mayar da mulki yankin Keffi."
Ana ci gaba da rigima kan magajin gwamna Sule a Adamawa
Sanata Ahmed Aliyu Wadada da aka zaba domin zama magajin Gwamna Abdullahi Sule. Hoto: Ahmed Aliyu Wadada.
Source: Facebook

Yadda gwamna ya zabi magaji cikin 'yan takara

Gwamna Sule ya bayyana cewa da yawa daga cikin masu neman takara sun cancanta amma dole ya duba mafi saukin samun nasara a cikinsu.

Ya ce akwai wanda ya kware a siyasa kuma amininsa ne amma duk da haka bai zabe shi ba saboda tabbatar da adalci.

Ya kara da cewa:

"Duk mutanen nan da suka fito gwamna wallahi duk sun cancanta, za su iya zama gwamna muna da injiniya, muna da likita da sauran su, idan aiki na zan bi sai in ba Farfesa Haruna.

Kara karanta wannan

An yi wa Gwamna karan tsaye bayan nuna magajinsa, Farfesa ya sha alwashi

"Akwai wadanda don iya siyasa, ya yi kakakin majalisa sau biyu, kuma babban akanta na ne ya san kudi da gwamnatina, kuma amini na ne."

Gwamna Sule ya ce Sanata Wadada ne a tunaninsa zai fi kawo kujerar gwamna cikin sauki ba tare da wahala sosai ba.

"Akwai kani na Wadada, wanda yanzu yana majalisar tarayya, akwai su da dama, amma na ce su je su zauna, su kawo min mutum daya.
"Daga baya, sai suka hada kai, su ka dawo gare ni, su ka ce kai gwamna mun san kana da adalci, ka je duk wanda ka dauka za mu goyi bayansa.
"Daga nan, na yi tuntuba, sai na ga wanda za a fi samun saukin cin zabe shi ne Wadada, sauran ma za su iya ci amma Wadada zai fi samun sauki."

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamnan jihar Nasarawa ya nada sabon sarki

A baya, an ji cewa an nada Alhaji Suleiman Ahmed-Eko a matsayin sabon Osu Ajiri na Udege, Sarki mai daraja ta daya a al’ummar Afo ta jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Malami ya umarci mabiyansa a Najeriya su ba 'yan bindiga lambar wayarsa idan aka sace su

Gwamnatin jihar Nasarawa ce ta tabbatar da nadin sabon Sarkin a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, 15 ga watan Afrilun 2026.

An haifi Ahmed Eko a ranar 2 ga watan Yuni, 1972, kuma ya kammala karatu a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.