Da Gaske Gwamnatin Amurka Ta Bankado Zargin Cin Hanci da Ake Yi wa Atiku?
- Wani sakon kafar sada zumunta ya yi ikirarin cewa gwamnatin Amurka ta fitar da sabon rahoton binciken cin hanci da rashawa kan Atiku Abubakar
- Bincike ya gano cewa takardar da sakon ya wallafa tsohon rahoto ne na kwamitin Majalisar Dattawan Amurka da aka fitar a 2010
- Rahoton ya zargi wasu mutane da harkokin karkatar da kudade, ciki har da Atiku, amma bai kai ga gurfanar da shi bisa wani laifi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yayin da zaben Najeriya na 2027 ke kara kusantowa, wani sako a kafar sada zumunta ya yi ikirarin nuna sabon binciken gwamnatin Amurka kan zargin cin hanci da rashawa.
Rahoton da yake yawo ya nuna bayanan majalisar Amurka kan zargin dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da cin hanci.

Source: Facebook
Zargin da ake yadawa kan Atiku Abubakar
Sakon, wanda aka wallafa a shafin X na SAsekome a ranar 25 ga Yuli, 2026 wanda a yanzu ya goge, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Amurka ta fitar da rahoton cin hanci da rashawa kan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.
Sakon ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da za su shiga wani sabon zangon zabe su yi watsi da Abubakar, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na African Democratic Congress, ADC.
Binciken kwa-kwaf ya fayyace gaskiyar zargin
Sai dai binciken AFP Fact Check ya nuna cewa wannan ikirarin yaudara ne, domin takardar da aka wallafa tsohon rahoto ne da aka fitar shekaru 16 da suka gabata.
Alamomin da ke cikin shafin farko na takardar sun nuna cewa an gabatar da ita ne a yayin wani zaman sauraron bayanai na ranar 4 ga Fabrairu, 2010.
Kwamitin bincike na dindindin na Majalisar Dattawan Amurka ne ya gudanar da zaman, karkashin Kwamitin Majalisar Dattawan kan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gwamnati.
Rahoton ya hada da zarge-zargen da suka shafi Teodoro Nguema Obiang Mangue na Equatorial Guinea, Atiku Abubakar, iyalan tsohon shugaban Gabon Omar Bongo da wasu jami’an gwamnatin Angola.

Source: Twitter
Yadda aka kasafta $40m asusun bankuna
Kwamitin ya gano cewa sama da dala miliyan 40 na kudaden kasashen waje da ake zargi an tura su cikin asusun bankunan Amurka ta hannun Jennifer Douglas, matar Atiku, tsakanin shekarun 2000 zuwa 2008.
Daga cikin kudaden akwai dala miliyan 14 da aka tura zuwa Jami’ar America ta hanyar wasu kamfanonin bogi da ke kasashen ketare.
Sakon ya kuma wallafa shafuka na 173 da 174 na rahoton, wadanda suka fi mayar da hankali kan Atiku Abubakar.
An gano cewa rahoton na 2010 an samar da shi ne karkashin jagorancin Sanata Carl Levin, dan jam’iyyar Democrat daga Michigan, wanda ya jagoranci kwamitin daga 2007 zuwa 2015.
Levin ya rasu a ranar 29 ga Yuli, 2021, yayin da wasu sanatoci suka jagoranci kwamitin bayan rasuwarsa.
A halin yanzu, Sanata Ron Johnson na jam’iyyar Republican daga Wisconsin ne ke jagorantar kwamitin, bayan ya karbi mukamin a watan Janairun 2025.
Saboda haka, binciken ya tabbatar da cewa ikirarin cewa takardar sabon binciken gwamnatin Amurka ce kan Atiku Abubakar ba gaskiya ba ne, domin tsohon rahoton Majalisar Dattawan Amurka ne na shekarar 2010.
Atiku ya ce ba zai yi takara a 2031 ba
An ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi magana kan lokacin da zai daina neman shugabancin Najeriya.
Atiku Abubakar wanda ya sha yin takarar shugaban kasa ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026.
Ya kuma bukaci masu katin zabe su fito su kada kuri’a tare da zama a rumfunan zabe domin tabbatar da an kirga kuri’unsu.
Asali: Legit.ng


