Ana Wata ga Wata: Trump Ya Kaddamar da Sabon Salon Yaki da Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da abin da ya kira mafi tsanantar matakin matsin tattalin arziki da kasarsa ta taba dauka kan Iran
- Trump ya yi barazanar hukunta duk wata kasa ko kamfani da zai ci gaba da bai wa Iran wata hanyar gudanar da harkokin kasuwanci ko kudi
- Matakin ya zo ne yayin da ake ci gaba da samun rashin cimma matsaya a tattaunawar kawo karshen yakin Amurka da Iran da ya dauki watanni biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington, Amurka – Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da wani sabon mataki na matsin tattalin arziki kan Iran, wanda ya bayyana a matsayin mafi tsauri da murkushewa da kasarsa ta taba dauka.
Trump ya ce matakin zai kara tsananta ware Iran daga harkokin tattalin arzikin duniya, yayin da ake ci gaba da samun tsaiko a tattaunawar kawo karshen yakin da ke tsakanin kasashen biyu.

Source: Facebook
Al Jazeera ta rahoto cewa Trump ya sanar da sabon matakin ne a wani sako da ya fitar ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026.
Gargadin Trump ga kasashe
Trump ya ce Iran ta kasa amfani da damar da aka ba ta domin cimma yarjejeniya, yana mai gargadin cewa Tehran za ta fuskanci wani matakin yakin tattalin arziki da wareta da ba a taba gani ba.
Ya kuma yi barazanar cewa duk wata kasa da za ta bai wa hukumomin kudi, kamfanoni, filayen jiragen sama ko hukumomin Iran wata damar ci gaba da gudanar da harkokinsu za ta fuskanci mummunan sakamakon tattalin arziki.
Trump ya ce:
"Duk kasar da ta bari cibiyoyinta na kudi, kamfanoni, filayen jiragen sama ko hukumomin gwamnati su bai wa Iran wata hanyar samun taimako, ita ma za ta fuskanci babbar matsalar tattalin arziki."
Ya ce dole ne a dakatar da safarar mai ba bisa ka'ida ba, musayar kudi, tura kudi, kamfanonin musaya, rajistar jiragen ruwa da kuma kamfanonin bogi da ake zargi da taimaka wa Iran wajen gudanar da harkokinta.

Source: Facebook
Rahoton ya ce Amurka ta riga ta kakaba takunkumi kan bangarorin man fetur, sufuri ta teku da kuma harkokin kudi na Iran, domin rage kudin shiga da Tehran ke samu daga fitar da makamashi.
Anadolu Agency ta wallafa cewa Amurka ta dauki matakan hana wasu kamfanoni, dillalai da jiragen dakon mai da ake zargi da taimaka wa Iran wajen sayar da man fetur a kasuwannin ketare.
Hoton taswirar Hormuz
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wata taswira a shafinsa, inda ya bayyana mashigar Tekun Hormuz a matsayin "Sabuwar Yankin Amurka."
Matakin ya biyo bayan rufe mashigar ta Hormuz da Iran ta yi, wadda hanya ce mai matukar muhimmanci wajen jigilar wani bangare mai yawa na man fetur na duniya.
Trump ya taba bayyana a baya cewa zai iya ayyana mashigar a matsayin mallakar Amurka, yayin da Iran ta mayar da martani cewa mashigar za ta ci gaba da kasancewa karkashin ikonta.
Asali: Legit.ng

