Kurunkus: Kwankwaso Ya Bayyana Ainihin Dalilin da Ya Sa Ya Amince Ya Zama Mataimakin Obi

Kurunkus: Kwankwaso Ya Bayyana Ainihin Dalilin da Ya Sa Ya Amince Ya Zama Mataimakin Obi

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya fito ya bayyana dalilin da ya sanya ya amince ya yi tafiya tare da Peter Obi a zaben shekarar 2027
  • Tsohon gwamnan na Kano ya ce abin da ya koya daga zaben 2023 ya taimaka masa wajen fahimtar Peter Obi, tare da tabbatar masa cewa za su iya yin aiki tare
  • Kwankwaso ya ce shawarar ta samu ne bayan tuntubar mambobin Kwankwasiyya Movement, magoya bayan jam'iyyar NNPP da Obidient Movement

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sanya ya amince ya zama abokin takarar Peter Obi.

Kwankwaso ya ce ya amince da zama abokin takarar Peter Obi a zaben 2027 ne saboda bukatar daidaiton kasa, adalci da kawo sauyin dimokuradiyya.

Sanata Kwankwaso ya yi magana kan takara da Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi wajen sauya sheka zuwa NDC Hoto: @Honsaifullahihassan
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da ya kasance bako a shirin Personality Interview Series na News Agency of Nigeria (NAN) a Abuja ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: 'Babu mai iya girgiza tikitin mu da Peter Obi a 2027'

Kwankwaso ya fahimci Peter Obi

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce abin da ya koya daga zaben 2023 ya taimaka masa wajen kara fahimtar Obi, kuma ya gamsu cewa za su iya yin aiki tare domin moriyar Najeriya.

“Mutane suna koyo a kullum, shi ya sa kwarewa take da matukar muhimmanci. A shekarar 2023, mun yi kokarin yin aiki tare, kuma a wancan lokacin ban san Peter Obi sosai ba."
“Amma a cikin shekaru hudu da suka gabata, na samu damar koyon abubuwa da dama kuma na fahimci cewa Peter mutum ne da zan iya yin aiki tare da shi,” in ji shi.

Kwankwaso ya ce bukatar bai wa Kudu damar ci gaba da rike shugabancin Najeriya na wani wa’adi bayan kammala wa’adin shekaru takwas na tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ma ta yi tasiri wajen yanke shawarar.

Tuntubar magoya bayan jam’iyyu

Ya ce an cimma matsayar ne bayan tuntubar mambobin Kwankwasiyya Movement, magoya bayan New Nigeria Peoples Party (NNPP) da kuma Obidient Movement.

Kara karanta wannan

Dino Melaye ya fadi 'yan siyasa 3 da suka sayar da PDP ga Tinubu kafin Wike ya karasa ta

A cewarsa, kungiyoyin sun yi imanin cewa Najeriya na bukatar tikitin takara mai daidaito wanda zai iya samun goyon baya daga Arewa da Kudu.

Karanta wasu labaran kan Kwankwaso

Kwankwaso ya yi magana kan Peter Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya taya Ademola Adeleke murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya taya gwamnan Osun, Ademola Adeleke, murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da hukumar zabe ta INEC ta gudanar.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar na NDC ya kuma taya al’ummar Osun murna saboda amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya da kuma sake tabbatar da abin da ya kira ikon zaɓin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng