Murtala Garo Ya Yi Akin Farko a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano

Murtala Garo Ya Yi Akin Farko a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano

  • Mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf wajen wani gagarumin taron siyasa awanni kadan da rantsar da shi
  • A ranar Talata, 6 ga watan Mayu na shekarar 2026 ne gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Garo a matsayin mataimakinsa bayan sun raba gari da Aminu AbdulSalam Gwarzo
  • Garo ya wakilci gwamna tare da wasu jiga-jigan APC da suka hada da tsohon shugaban jam'iyya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Mataimakin gwamnan Kano, Hon Murtala Sule Garo ya karbi ragamar aiki da fara wakiltar gwamna Abba Kabir Yusuf.

Garo ya wakilci gwamna a wajen taron karɓar tsohon Sanatan Kano ta Arewa, Bello Hayatu Gwarzo, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani da Murtala Garo ya zama sabon mataimakin gwamnan Kano

Murtala Sule Garo ya wakilci gwamnan Kano
Murtala Sule Garo yayin tarbar Bello Hayatu Gwarzo zuwa APC a Kano Hoto: Gida Gida TV
Source: Facebook

Freedom Radio ta wallafa a shafinta na Facebook cewa taron ya gudana ne a garin Gwarzo wanda ya samu halartar dimbin magoya baya a jihar Kano.

Murtala Sule Garo ya wakilci gwamnan Kano

Abba Gida Gida TV ta wallafa a shafin na Facebook cewa Bello Hayatu Garzo ya sauya sheƙa da ake ganin yana matuƙar muhimmanci ga siyasar jihar Kano.

Mataimakin gwamna Murtala Sule Garo ne ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron, inda ya bayyana goyon bayan gwamnatin jihar Kano ga tsarin zaman lafiya da hadin kai a siyasa.

Manyan APC sun raka Garo taro Hayatu Gwarzo
Malam Ibrahim Shekarau, Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakin gwamna Murtala Sule Garo da shugaban APC a Kano Umar Haruna Doguwa wajen tarbar Hayatu Gwarzo Hoto: Gida Gida TV
Source: Facebook

Tsofaffin gwamnonin Kano da suka hada da Malam Ibrahim Shekarau da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, sun halarci taron, tare da shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, da sauran manyan jami’an jam’iyyar.

Sun bayyana cewa wannan sauyin sheƙa zai ƙara wa jam’iyyar APC ƙarfi da tasiri, musamman a lokacin da jam’iyyun siyasa ke shirin tunkarar zaɓukan 2027 a Najeriya.

Kara karanta wannan

A karon farko, Ganduje ya amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

APC na kara fadada tasirinta a Kano

Rahotanni sun ce wannan sauyin sheƙa ya ƙara nuna irin yadda jam’iyyar APC ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinta a Arewacin Najeriya, musamman a jihar Kano da ke da matuƙar muhimmanci a siyasar ƙasar.

A jawabansu daban-daban, manyan bakin da suka halarci taron sun jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin ‘yan jam’iyya, tare da bayyana cewa shigowar Sanata Gwarzo APC zai kara wa jam’iyyar karfi.

Taron ya kuma zama wata dama ta tattaunawa kan shirye-shiryen siyasa gabanin zabukan shekarar 2027, inda aka bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa manufofin APC.

An rantsar da Garo a Kano

A baya, mun wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Mutala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna a wani taro da aka shirya a ranar Talata, 5 ga watan Mayu 2026.

Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje da Malam Ibrahim Shekaru na cikin manyan bakin da suka halarci bikin rantsar da Garo yayin da sha rantsuwar zama mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan

An rantsar da mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, manyan jiga jigai sun halarta

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar dokokin Kano karkashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore ta tantance tare da amincewa da shi bayan kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya yi murabus.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng