2027: Mata 6 da Suka Nuna Sha’awar Neman Takarar Gwamna a Najeriya
Yayin da ake ta shirye-shiryen zaben shekarar 2027, an samu mata da dama a Najeriya da suka nuna sha'awar fitowa takarar gwamna.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dukkan matan da aka lissafo sun fito ne a karkashin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a jihohinsu daban-daban a kasar.

Source: Facebook
Rahoton The Guardian ta ruwaito cewa daga cikin matan da suka nuna sha'awar takarar akwai guda biyu daga Kwara da kuma biyu daga Ogun.
Har ila yau, daya daga cikin matan ta fito ne daga jihar Gombe karkashin APC yayin da aka sake samun wata daga jihar Nasarawa.
Legit Hausa ta yi bincike tare da jero matan da suka nuna sha'awar rike kujerar da ta fi kowace girma a jihohinsu.
1. Sa’adatu Sa’ad-Mustapha - Jihar Gombe
Hajiya Sa’adatu Sa’ad-Mustapha ta zama mace tilo da ta fito takarar gwamna a Gombe domin zaɓen 2027, cewar Punch.
Sa’ad-Mustapha, tsohuwar kwamishiniyar muhalli da albarkatun dazuzzuka, ta mika takardar bayyana aniyarta a sakatariyar APC ta jihar.
Daga bisani, Sa'adatu ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar da Gwamna Inuwa Yahaya ya fitar watau Jamilu Isyaku Gwamna kamar yadda Isma'ila Uba Misilli ya yada a Facebook.

Source: Facebook
2. Fatima Abdulahi - Jihar Nasarawa
Yar siyasa a jihar Nasarawa, Fatima Abdullahi ta nuna sha'awar tsayawa takara domin a fafata da ita a zaben gwamna a 2027.
Fatima ta ce bayyana aniyarta na tsayawa takara duk da Gwamna Abdullahi Sule ya nuna wanda ya ke son ya gaje shi watau Sanata Ahmed Wadada.
Rahoton BusinessDay ya ce Fatima ta bayyana cewa tana da yakinin za ta yi nasara saboda al'umma ne za su yanke hukunci.
3. Aisha Ahman-Pategi - Jihar Kwara
Tsohuwar kwamishiniyar kananan hukumomi da harkokin masarautu a Kwara, Aisha Ahman-Pategi, ta zama mace ta farko da ta bayyana aniyar tsayawa takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Aisha Ahman-Pategi, wadda aka fi sani da “Mama Oyoyo”, ta shiga takarar kujerar gwamnan jihar a hukumance, cewar Leadertship.
Da take jawabi ga dumbin magoya bayanta, Ahman-Pategi ta ce bayyana aniyarta ya zo ne a lokacin da jarumtaka ta haɗu da manufa.

Source: Facebook
4. Musliat Yetunde Bello - Jihar Kwara
Hajiya Musliat Yetunde Bello, ta ayyana neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a Kwara a zaɓen 2027.
Yetunde ta ce tana da burin dorawa kan nasarorin da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya samu, tare da ƙarfafa shigar mata cikin shugabanci, cewar Vanguard.
Da take magana da manema labarai a Ilorin, ta bayyana cewa burinta na takara ya samo asali ne daga hidimar jama’a da kuma ƙoƙarin ƙara yawan mata masu shiga harkokin shugabanci da bunƙasa tattalin arziki.
5. Iyabo Obasanjo - Jihar Ogun
Sanata Iyabo Obasanjo ta koma APC tare da bayyana aniyarta ta tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Tsohuwar sanatar ta ce matsin lambar magoya baya ne ya sa ta dawo siyasa bayan kusan shekaru 15 da watsar da ita.
Iyabo ta jaddada cewa APC ce 'gidanta na gaskiya', ta kuma yi watsi da komawa PDP ko ADC masu adawa a Najeriya.
Daga bisani, an yi zama a jihar domin samun damar tsayar da dan takara inda aka amince a ba Sanata Solomon Adeola.

Source: Twitter
6. Modele Sarafa-Yusuf - Jihar Ogun
Tsohuwar yar jaridar wasanni, Modele Sarafa-Yusuf, ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar gwamnan Ogun a zaɓen 2027.
Haka na cikin wata budaddiyar wasika da ta wallafa a shafinta na X, inda Sarafa-Yusuf ta sanar da kudirinta na neman kujerar gwamna.
Dattijuwar ta tabbatar da cewa takararta za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jam’iyya.
Ta danganta hakan da abin da ya faru a 2022 lokacin da ta amince da shan kaye ba tare da haddasa rikici ko tada husuma a cikin jam’iyya ba.
Gwamna Inuwa ya nuna magajinsa a Gombe
Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ta tsayar da dan takarar gwamnan domin tunkarar zaben shekarar 2027.
APC ta tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin dan takararta na maslaha a zaben shekarar 2027 da ake fuskanta.
Hakan na nufin tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Ali Pantami, da sauran masu neman takarar gwamna a APC, ba za su samu tikiti ba idan har ba zaben fidda gwani aka yi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


