Abin da Atiku Zai Yi cikin Kwana 100 don Magance Rashin Tsaro idan Ya Zama Shugaba
- Atiku Abubakar ya bayyana shirin da yake da shi kan magance matsalar rashin tsaro idan ya samu nasarar zama shugaban kasar Najeriya
- Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce gazawar shugabanci ce ta sa aka kasa shawo kan matsalar tsaro
- Atiku ya kuma yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na African Democratic Congress (ADC) a zaben 2027, ya bayyana shirinsa kan matsalar rashin tsaro.
Atiku Abubakar ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya, zai dauki muhimman matakai domin kawo karshen rashin tsaro a kasar.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026 wadda ya sanya a shafinsa na Facebook.
Ayyukan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, ‘yan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yamma, ayyukan da IPOB ke yi a Kudu maso Gabas da kuma sace-sacen mutane a Kudu maso Yamma, na daga cikin kalubalen tsaro da suka yi sanadin mutuwar dubban ‘yan Najeriya tare da raba wasu dubban da muhallansu.
Abin da Atiku zai fara yi
Atiku ya ce daya daga cikin abubuwan da zai fara yi a cikin kwanaki 100 na farko da ya hau mulki shi ne kara yawan jami’an tsaro tare da samar musu da isassun kayan aiki.
“Abin da zan yi a cikin kwanaki 100 na farko a kan mulki domin magance rashin tsaro shi ne kara yawan jami’an tsaro da samar musu da isassun kayan aiki."
“Boko Haram ta fara ne a Yobe. A lokacin shugaban kasa ya kira ni ya gaya mini cewa akwai babbar matsala, ya tambaye ni abin da ya kamata a yi. Na ba shi shawarar ya tara dukkan shugabannin hukumomin tsaro."
“Lokacin da suka zo, na ce ya tambaye su ko dai su shawo kan matsalar ko kuma su yi murabus. Amma yanzu, gazawar shugabanci ce ta sa ba a kiran su.”
Atiku ya yi magana kan sojoji
Da yake magana kan zanga-zangar da wasu tsofaffin sojoji suka gudanar a baya-bayan nan, Atiku ya ce ba a biyan su hakkokinsu duk da dimbin albarkatun da Najeriya ke da su.
Ya zargi karkatar da kudaden gwamnati da kuma satar dukiyar jama’a da haddasa wannan matsala.
Alkawarin dawo da tallafin man fetur
Sai dai Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce cire tallafin man fetur bai inganta rayuwar ‘yan Najeriya ba.

Source: Facebook
Lokacin da Atiku zai daina yin takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi maganar lokacin daina neman kujerar shugabancin Najeriya.
Atiku Abubakar ya ce ba zai sake neman takarar shugaban kasar Najeriya ba idan ya sha kaye a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

