NDC Ta Kashe Gobarar da Ta Taso Mata a Kano, An Biya Bukatar Shugaban Jam'iyya

NDC Ta Kashe Gobarar da Ta Taso Mata a Kano, An Biya Bukatar Shugaban Jam'iyya

  • NDC ta warware rikicin shugabanci a Kano, bayan wasu kalamai da shugaban jam'iyyar Hon. Husaini Isah Mai Riga ya fara jawo rikici
  • Hon Mai Riga ya fito kafafen yada labarai yana zargin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigo NDC da mutanensa kuma za a tura su gefe
  • Shugaban ya bayyana cewa ba za su taba lamunta ba a yi masu abin da ya kira ture kaza kwashe kwai gabanin zaben 2027 ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam’iyyar NDC ta kawo ƙarshen rikicin shugabanci da ya ɓarke a reshen ta na jihar Kano, inda ta sake jaddada Hon. Husaini Isah Mai Riga a matsayin shugaba a jihar.

Rikicin ya samo asali ne bayan shigar tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai, an tayar da hargitsi a wurin taron jam'iyyar NDC a Enugu

NDC ta tattara kan 'ya'yanta a Kano
Peter Obi, Rabi'u Musa Kwankwaso tare da jagoran NDC a Abuja Hoto: NDC Kwankwasiyya Movement
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan al'amari ya fara jawo rashin jituwa a tsakanin 'yan jam'iyyar, musamman bayan Mai Riga ya yi zargin za a nuna masu wariya.

Yadda aka zauna kan batun NDC

Trust Radio ta wallafa cewa tun farko, Mai Riga ya tsaya tsayin daka cewa ya samu shugabanci ne bisa ƙa’ida, yana mai jaddada cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba sai an bi hanyoyin da suka dace.

Wannan ta jawo ya fito da wasu maganganu da ke cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai yi masa dole, shi kuma ba zai taba lamunta ba.

NDC ta biya bukatar Mai Riga a Kano
Aisha Binani, Peter Obi, Serieke Dickson, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran yan NDC a Abuja Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Twitter

A karshe, shugabancin jam’iyyar na ƙasa ya kira wani muhimmin taro na musamman a ranar Talata 5 ga watan Mayu na shekarar 2026 ƙarƙashin jagorancin Sanata Seriake Henry Dickson domin lalubo mafita ga matsalar.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daga ciki har da Kwankwaso da mataimakin shugaban NDC na shiyyar Arewa maso Yamma, Engr. Muhammad Sabo Bakin Zuwo.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya hango matsala tun yanzu a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi

NDC ta warware matsalar jam'iyya a Kano

Majiyoyi daga cikin NDC sun bayyana cewa Kwankwaso ya amince da wannan matsaya, inda aka bar Mai Riga a kan mukaminsa, yayin da aka bai wa ɓangaren Kwankwaso wasu muƙamai a tsarin shugabanci domin daidaita al’amura.

Bayan kammala zaman, Mai Riga ya nuna godiya ga shugabannin jam’iyyar na ƙasa da kuma al’ummar Kano bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin rikicin.

Haka kuma, ya nemi afuwar duk wanda ya ɓata wa rai a kwanakin baya, yana mai cewa sakamakon da aka samu ya nuna hikimar shugabannin jam’iyyar.

A cewarsa, an amince a bai wa ɓangaren Kwankwaso 60% na tsarin shugabanci a Kano, yayin da shi kuma zai ci gaba da zama shugaban jam’iyyar.

Guguwa ta tunkaro NDC

A baya, kun samu labarin cewa daya daga cikin manyan jam'iyyar ADC, Dr. Umar Ardo ya ce zai ci gaba da shari’a kan sahihancin rajistar jam’iyyar adawa ta NDC da manyan yan siyasa suka koma a bayan nan.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya gayyaci Atiku zuwa NDC bayan sauya shekar Kwankwaso da Obi

Ya zargi NDC da rashin cika sharuddan rajista na INEC jim kadan bayan jagororin siyasa irinsu Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun shige ta yayin da aka fara shirye-shiryen siyasar 2027.

Dr. Umar Ardo wanda makusancin Alhaji Atiku Abubakar ne kuma jigo a ADC ya bayyana cea ba zai zauna haka kawai ya ga ana rashin gaskiya ba tare da ya dauki matakin da ya dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng