Ana Kaɗa Ƙuri'a a Osun, Ƴan Sanda Sun Faɗi Tanadinsu kan Zaben Bauchi

Ana Kaɗa Ƙuri'a a Osun, Ƴan Sanda Sun Faɗi Tanadinsu kan Zaben Bauchi

  • Rundunar ’yan sandan Bauchi ta shaidawa mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu gabanin zaben da za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa
  • Ta tabbatar wa mazauna jihar Bauchi cewa an gama shiri na samar da cikakken tsaro kafin 17 ga Agusta, 2026 da sauran muhimman lokuta
  • Rundunar ta ce ta tura jami’anta zuwa wurare daban-daban domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma kayan zaɓe a dukkan ƙananan hukumomi 20 na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar wa mazauna jihar cewa ta tanadi isasshen tsaro domin tabbatar da gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi cikin lumana a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ne ya bayar da tabbacin cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya sanya wa hannu tare da rabawa manema labarai ranar Asabar 15 ga watan Agusta 2026.

Kara karanta wannan

An tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC yayin da ake shirin zaben gwamnan Osun

Yan sandan Bauchi sun shirya tsaf, ana jiran zaben kananan hukumomi
Wasu daga cikin jami'an yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa rundunar ta ce ta shirya cikakken tsarin tsaro da nufin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, gaskiya da ba tare da tangarda ba a dukkan ƙananan hukumomi 20 na jihar.

Yan sanda sun shirya wa zaben Bauchi

A ruwayar jaridar Punch, an tura jami’an ’yan sanda zuwa muhimman wurare daban-daban a jihar domin ƙarfafa tsaro, tare da kare rayuka, dukiyoyi da kayan zaɓe kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.

Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci tashin hankalin zaɓe, satar akwatin zaɓe, daba, saye ko sayar da ƙuri’u, tsoratar da masu zaɓe ko kuma duk wani yunkuri na kawo cikas ga tsarin zaɓe ba.

Yan sandan Bauchi sun ce za a yi zabe lafiya lau
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sanarwar ta ce:

“Za a kama tare da gurfanar da masu aikata laifukan, masu ɗaukar nauyinsu da abokan hulɗarsu, ba tare da la’akari da matsayinsu ko ƙungiyar da suke goyon baya ba."

Yan sanda sun yi alkawari a Bauchi

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Kwamishinan ’yan sandan ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa jami’an da aka tura aikin zaɓen za su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam da bin dokokin ƙasa da ke aiki.

Rundunar ta buƙaci mazauna jihar Bauchi su fito su kaɗa ƙuri’unsu ba tare da fargaba ba, sannan ta shawarce su da su gaggauta kai rahoton duk wani abin da suka yi zargin yana da nasaba da aikata laifi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Rundunar ’yan sandan ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da samar da yanayi mai aminci da tsaro a duk tsawon lokacin gudanar da zaɓen.

An fara wallafa sakamakon zaben Osun

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta fara dora sakamakon zaben gwamnan jihar Osun a shafinta na yanar gizo (IReV) a yayin da ake ci gaba da dakon sauran.

Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa zuwa yanzu, INEC ta wallafa sakamakon rumfunan zaɓe 1,011 cikin 3,763 a shafinta na IReV wanda a nan ne aka tattara abin da kowane dan siyasa ya samu daga rumfuna.

Sakamakon da aka dora a shafin INEC ya kai kashi 26.87 cikin 100 na jimillar sakamakon da ake jira daga rumfunan zaben Osun wanda ya ke kara daukar hankali musamman bayan zarge-zargen tashin hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng