Bayan Shigar Kwankwaso da Obi, NDC Ta Fadi 'Yan Takarar da Za Ta Tsaida a 2027

Bayan Shigar Kwankwaso da Obi, NDC Ta Fadi 'Yan Takarar da Za Ta Tsaida a 2027

  • Sabuwar jam'iyyar NDC mai adawa na ci gaba da samun tagomashi tun bayan da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi suka sauya sheka zuwa cikinta
  • Bayan sauya shekar tsofaffin 'yan takarar shugaban kasar a zaben 2023, NDC ta bayyana cewa ta samu karin mambobi wadanda suka yi ta tururuwa zuwa cikinta
  • Hakazalika, jam'iyyar NDC ta dauko batun 'yan takarar da za ta tsaida domin fafatawa a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Calabar, jihar Cross River- Jam’iyyar NDC mai adawa ta fara magana kan 'yan takarar da za ta tsaida a babban zaben shekarar 2027.

Jam'iyyar NDC reshen jihar Cross River ta bayyana cewa za ta tsayar da nagartattun ’yan takara a babban zaɓen 2027.

NDC za ta tsaida 'yan takara a 2027
Jagoran NDC na kasa na jawabi wajen karbar Kwankwaso da Peter Obi Hoto: @iamHSDickson
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa shugaban jam’iyyar, Mista Goddie Akpama, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai ranar Talata, 5 ga watan Mayun 2026 a birnin Calabar.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya hango matsala tun yanzu a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi

Shigar Kwankwaso da Obi zuwa NDC

Akpama ya ce NDC ta samu gagarumin ci gaba tun bayan da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka shiga jam’iyyar.

Ya siffanta jam’iyyar a matsayin wani rukunin siyasa mai haɓaka, inda ya bayyana cewa ta ƙara samun ƙarfi da tagomashi a cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

“NDC na wakiltar wata sabuwar alkibla ce ga Najeriya, jam’iyyar tana nan daram kan ƙudurinta na samar da shugabanci na gari."
“Jam’iyyar tana tuntuɓar muhimman jiga-jigan siyasa domin ƙarfafa tsarinta da kuma karɓuwarta a matakin ƙasa."

- Goddie Akpama

NDC na kokarin samar da hadin kai

Ya bayyana cewa saɓanin ra’ayi na cikin gida wani ɓangare ne na tsarin dimokuraɗiyya, kuma hakan ba zai raunana ƙudurin jam’iyyar ba, rahoton Daily Post ya nuna hakan.

Shugaban ya ce NDC tana gina haɗin kai a tsakanin mambobi da masu ruwa da tsaki domin hana afkuwar rikicin cikin gida.

Akpama ya ƙara da cewa jam’iyyar tana aiki don ƙarfafa tushenta, da kuma sanya kanta a matsayin sahihin dandamalin siyasa wanda ya ƙuduri aniyar karɓar shugabanci a matakin ƙasa da na jiha.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya gayyaci Atiku zuwa NDC bayan sauya shekar Kwankwaso da Obi

NDC za ta tsaida nagartattun 'yan takara
Kwankwaso da Peter Obi wajen sauya shekarsu zuwa NDC Hoto: @iamHSDickson
Source: Facebook

Wadanne 'yan takara za ta tsaida?

“Mu ba wasa muke yi ba, za mu tabbatar da cewa dukkan muƙaman zaɓe mun cika su da ’yan takara waɗanda suke da nagarta da mutunci."

- Goddie Akpama

Ya bayyana cewa babban abin da jam’iyyar ta sa a gaba a yanzu shi ne ƙarfafa tsarinta da kuma tabbatar da haɗin kan mambobinta.

Buba Galadima ya bukaci Atiku ya shiga NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a sabuwar jam'iyyar NDC, Buba Galadima, ya mika kokon bararsa ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Buba Galadima ya bukaci Atiku Abubakar, da ya shiga jam’iyyar NDC, inda ya yi gargadin cewa za a iya dora masa alhakin gazawar hada kan 'yan adawa gabanin babban zaben 2027.

A cewar tsohon jigon na jam'iyyun ADC da NNPP Mafi yawa daga cikin 'yan adawa na ci gaba da yin tururuwa zuwa jam'iyyar NDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng