Matsala Ta Kunno Kai, An Tayar da Hargitsi a Wurin Taron Jam'iyyar NDC a Enugu
- Wasu da ake zargin 'yan dabar siyasa ne sun kai farmaki wurin taron zaben shugabannin jam'iyyar adawa ta NDC ta reshen jihar Enugu
- Rahotanni sun nuna cewa an fara taron cikin lumana, amma daga bisani ya rikida zuwa rigima lokacin da aka zo matakin sauke tsofaffin shugabanni
- Duk da rikicin da ya auku, jiga-jigan NDC sun samu nasarar kariaa taron tare da zaben Johnpaul Anih a matsayin shugaban jam'iyya na Enugu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu, Nigeria – Taron jam’iyyar NDC a jihar Enugu ya rikide zuwa rikici a ranar Litinin, bayan wasu da ake zargi da ‘yan daba ne sun mamaye wajen tare da tarwatsa zaman.
Hakan dai na zuwa ne awanni kadan bayan Peter Obi, wanda ya fito daga shiyyar Kudu masi Gabas, ya koma jam'iyyar NDC tare da tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Source: Original
The Nation ta ce taron, wanda aka gudanar a dakin taro na Aborigene Hall a cikin birnin Enugu, na cikin tarukan da NDC ta shirya gudanarwa a dukkan jihohin kasar nan da Abuja a ranar 5 ga Mayu, 2026.
Yadda rikici ya barke a taron jam'iyyar NDC
An ruwaito cewa an fara taron lami lafiya kuma komai na tafiya yadda ya kamata har sai da aka gabatar da kudirin rusa kwamitin rikon kwarya na jiha.
A nan ne aka ce wasu mutane da ake zargi da ‘yan daba suka shigo, suka kwace iko da wajen taron tare da umartar mahalarta da su fice.
Wani ganau ya ce:
“Yan daban sun fara da cire tutoci sannan suka umurci kowa da ya bar wajen.”
Jigon NDC ya fadi wadanda ake zargi
Duk da cewa ba a gano wadanda ke da hannu a lamarin ba, wani dan jam’iyyar NDC ya yi zargin cewa rikicin na da alaka da wasu sababbin shiga jam’iyyar da ke kokarin kwace tsarin jagoranci.
"Sun shigo jam’iyyar NDC ne jiya Lahadi a taron sauya shekar da aka gudanar, amma yanzu suna son kwace komai," in ji shi.
ADC ta zabi sababbin shugabanni a Enugu
Duk da wannan matsala, an ci gaba da taron a karkashin tsauraran matakai, inda aka kammala da zaben Dr. Johnpaul Anih a matsayin sabon shugaban jam’iyyar NDC na jihar Enugu.
Bayanai sun nuna cewa Dr. Anih ya samu nasara ne ta hanyar tsarin sulhu da jam’iyyar ta amince da shi.
Dr. Anih, wanda tsohon mai ba gwamnan Enugu shawara kan harkokin matasa ne, ya gode wa ‘yan NDC tare da alkawarin karfafa jam’iyyar a jihar.

Source: Facebook
Ya kuma bukaci dukkan mambobi da su hada kai su zama tsintsiya daya domin ci gaban jam’iyyar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da Dr. Sebastian Okafor a matsayin sakatare, Mrs. Florence Anigbo a matsayin shugabar mata, da Clinton Ogbonna a matsayin shugaban matasa.
An bukaci Atiku ya koma NDC
A wani labarin, kun ji cewa Buba Galadima ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da ya baro ADC, ya koma jam'iyyar NDC.

Kara karanta wannan
NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya
Galadima ya bayyana cewa tuni alkiblar siyasa ta fara karkata zuwa ga wani dandamali na hadakar adawa, inda fitattun mutane da dama suka riga suka shiga cikin NDC.
Ya bukaci Atiku da ya bi wannan tafarkin, inda ya jaddada cewa hadin kai shi ne kadai sahihiyar hanyar da za a iya fuskantar gwamnati mai ci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

