'Yan Takarar Shugaban Kasa 3 Sun Hada Kai domin Kwace Mulki daga Hannun Tinubu a 2027

'Yan Takarar Shugaban Kasa 3 Sun Hada Kai domin Kwace Mulki daga Hannun Tinubu a 2027

  • ‘Yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun Accord, AAC da SDP sun amince da haɗa ƙarfinsu domin samar da hadaka a zaɓen 2027
  • Gbenga Olawepo-Hashim, Omoyele Sowore da Adewole Adebayo sun cimma matsayar ne bayan wata ganawa da suka yi a Fatakwal
  • ‘Yan siyasar sun ce muradin ƙasa ya kamata ya kasance a sahun gaba fiye son zuciyar kowane ɗan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - ‘Yan takarar shugaban ƙasa sun amince du kulla kawance domin tunkarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a babban zaben 2027.

Yan takarar na jam’iyyun Accord, AAC da SDP sun amince da yin aiki tare domin samar da ƙarfi na bai ɗaya na dimokuraɗiyya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gbenga Olawepo-Hashim
Dan takarar shugaban kasa na Accord, Gbenga Olawepo-Hashim da Prince Adewole Adebayo Hoto: Gbenga Olawepo-Hashim
Source: Facebook

Dr Gbenga Olawepo-Hashim na Accord, Omoyele Sowore na AAC da Prince Adewole Adebayo na SDP ne suka cimma wannan matsaya bayan wata ganawa da suka yi a Fatakwal a ƙarshen mako, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Ba jira': Kwankwaso ya fadi tanadin NDC wajen nada mukamai idan an zabe ta

A yayin ganawar, ‘yan takarar sun tattauna kan dimokuraɗiyyar Najeriya, tattalin arziki da tsaro.

Sun nuna damuwa kan yadda ake tattara ikon siyasa a hannun wasu, raunana cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma rage damar nuna adawa ta gaskiya.

Sun yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar haɗarin sauyawa daga tsarin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama zuwa wani yanayi da suka bayyana da cewa “nadin sarauta da aka ɓoye a matsayin zaɓe”.

‘Yan takara 3 sun shirya haɗa ƙarfi a 2027

Shugabannin sun amince da daidaita ƙarfinsu na siyasa domin bai wa ‘yan Najeriya wani dandamalin siyasa a zaɓen 2027.

Kawancen da ake shirin kafawa zai nemi haɗa ma’aikata, matasa, mata, ƙwararru, ‘yan kasuwa, ƙungiyoyin farar hula da ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙabila, addini, yanki da siyasa.

‘Yan takarar sun ce har yanzu ba su kammala yanke shawarar tsarin kawancen, yadda za a gudanar da shi da kuma wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasar da za su marawa baya.

Kara karanta wannan

Bayan turmusa ta a zaɓen Osun, APC ta faɗi matakin da za ta ɗauka nan gaba

"Muradin ƙasa dole ne ya fi son zuciyar mutum ta siyasa muhimmanci," in ji su.
Omoyeke Sowore.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

An bukaci gwamnati ta kyale Sowore

‘Yan takarar sun kuma nemi a kawo ƙarshen abin da suka kira tsangwamar Omoyele Sowore ta fuskar shari’a da siyasa saboda ayyukansa na siyasa,cewar rahoton Leadership.

Sun nuna damuwa kan zargin yunƙurin da wasu mutane ke yi a cikin hukumomin tsaro, hukumomin zaɓe, ɓangaren shari’a, majalisa da zartarwa na raunana jam’iyyun adawa,

G100 ta shsirya hada kan yan adawa

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar G100 ta bukaci shugabannin adawa su hada kai su tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya a zaben 2027.

Ta bayyana cewa ba za a samu cikakken gyara ba sai an samu bangaren adawa mai karfi, hadin kai da kuma kishin kasa wanda zai rika dorawa gwamnati alhakin ayyukanta.

Kungiyar ta bukaci manyan shugabannin adawa a Najeriya da su jingine duk wani banbanci da burikansu na kashin kai, su hada kai wuri guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262