'Ba Su da Sauran Mamora a Siyasa': Kwankwaso Ya Ce Ta Karewa Su Ganduje a Kano

'Ba Su da Sauran Mamora a Siyasa': Kwankwaso Ya Ce Ta Karewa Su Ganduje a Kano

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana game da asirin tsofaffin gwamnonin Kano, Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf
  • Kwankwaso ya zargi Ganduje da barin tsarin siyasar da suka gina tare, yana mai cewa hakan ne ya jawo masa koma baya a siyasa duk da ya shugabanci APC
  • Tsohon gwamnan ya kuma ce Abba Yusuf ya nisanta kansa daga tawagar siyasar da ta taimaka masa wajen zama gwamna, tare da kokarin maye gurbinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya tabo tsoffin gwamnonin jihar.

Ya bayyana cewa Sanata Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, sun kammala siyasarsu a Kano.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Kwankwaso ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ya amince ya zama mataimakin Obi

Kwankwaso ya soki Ganduje da Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Umar Ganduje, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature D-Tofa,Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2026, inda ya yi tsokaci kan makomar wasu daga cikin tsoffin abokan siyasarsa da suka rabu da shi.

Kwankwaso ya tabo tsofaffin gwamnonin Kano

Daily Post ta kawo labarin cewa Kwankwaso ya ce nasarar siyasa da aka gina bisa “cin amana” ba za ta dore ba, yana mai cewa kwarewarsa a siyasa cikin sama da shekaru 25 ta tabbatar masa da hakan

A kalamansa:

“Ba za ka iya yin nasara da cin amana ba. Ban taba ganin wanda ya yi hakan ya yi nasara ba. Yanzu shekaru kusan 25 kenan. Idan na tambaye ka, na tabbata ba za ka san shi ba; an manta da shi a siyasa."

Abin da Kwankwaso ya ce kan Ganduje

Kwankwaso ya yi tsokaci musamman kan Abdullahi Ganduje, wanda ya kasance mataimakinsa na tsawon shekaru takwas kafin ya gaje shi a matsayin gwamnan Kano a shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: 'Babu mai iya girgiza tikitin mu da Peter Obi a 2027'

Ya ce siyasar Ganduje za ta kasance mai karfi idan ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar da suka gina tare, yana mai cewa rabuwa da shi ce ta fara janyo koma bayan tsohon gwamnan.

Kwankwaso ya kara da cewa Ganduje zai iya samun karin mutunci a Kano da sauran wurare idan ya ci gaba da kasancewa mai biyayya ga tsarin siyasar da suka gina tare.

Kwankwaso ya ce siyasar su Shekarau ta mutu a Kano
Abdullahi Umar Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Ibrahim Shekarau/Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya kuma soki Gwamna Abba Yusuf bisa zargin cewa ya yi watsi da mutanen da suka yi aiki tukuru wajen ganin ya zama gwamnan Kano.

Kwankwaso ya ce zabin Abba Yusuf a matsayin dan takararsa ya samo asali ne, a wani bangare, daga bukatar kauce wa sake faruwar abin da ya ce Ganduje ya yi.

Ya ce:

“Ya bar mu, amma ba ya tare da Ganduje yanzu. Yana tsakani ne, domin ba na tunanin yana son wani ya kira shi Dan Gandujiyya."

Abin da Kwankwaso ya ce kan 2027

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce hadin gwiwarsa da Peter Obi ya samar da tikitin mai karfin gaske wanda ya fi karfin sauran yan siyasa a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Ba abu ne mai sauki ba"; Gwamna Abba ya fadi wahalar mulkin Kano

Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin inuwar NDC ya kuma bayyana dalilinsa na fadin cewa sun fi kowa karfi saboda wadansu dalilai da ya bayyana.

Ya ce karfin Obi a Kudancin Najeriya da tasirinsa a Arewa za su taimaka wajen samar da gagarumin hadin kan kasa a zaben shugaban kasa na 2027 idan lokacin kada kuri'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng